Sabon Rikici Ya Barke a Wasu Garuruwan Sokoto, An Gwabza da Sulhu Ya Rushe

Sabon Rikici Ya Barke a Wasu Garuruwan Sokoto, An Gwabza da Sulhu Ya Rushe

  • Akalla mutum 10 suka jikkata bayan rikicin gona ya rikide zuwa tashin hankali tsakanin mazauna garuruwan Chirif Magaji da Chirif Dikko
  • Rahotanni sun nuna cewa bangarorin biyu sun shafe kusan shekara uku suna takun saka kan hakkin noma da mallakar gonar da ake rikici a kanta
  • Jami’an tsaro sun shiga tsakani domin dawo da zaman lafiya yayin da aka kai wadanda suka jikkata asibitoci daban-daban na Sokoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Sokoto - Akalla mutane 10 ne suka samu raunuka bayan wata takaddama kan mallakar gona ta rikide zuwa rikici tsakanin garuruwan Chirif Magaji da Chirif Dikko da ke karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto.

Bayanai sun nuna cewa bangarorin biyu sun dade suna samun sabani kan wanda ya dace ya mallaka da kuma noma gonar da ake takaddama a kanta, lamarin da ya shafe shekaru kusan uku yana faruwa.

Kara karanta wannan

Sabon kudiri: Ana son shugaban kasa ya dawo yin shekara 6 ba tazarce a Najeriya

An samu tashin hankula da rikici ya barke a wasu garuruwan Sokoto.
Taswirar jihar Sokoto da ke a Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rikici ya barke a garuruwan Sokoto

Rahoto na musamman da Daily Trust ta fitar sun bayyana cewa rikicin ya tsananta ne a ranar Talata bayan wasu mazauna daya daga cikin garuruwan sun je domin share gonar da ake ce-ce-ku-ce a kanta.

Wata majiya daga bangaren tsaro ta ce mutanen sun fada tarkon wasu da ake zargin sun zo dauke da bindigogin toka da makamai masu kaifi.

“Mun samu bayanin gaggawa cewa rikici ya barke tsakanin bangarorin biyu, nan take jami’an tsaro suka isa wurin domin dakile rikicin da dawo da zaman lafiya,” in ji majiyar.

Ta kara da cewa maharan sun bude wuta, wanda hakan ya janyo jikkatar mutum shida daga cikin wadanda suka je aikin gonar.

Mutane sun samu raunuka

Bayan samun labarin harin, wasu daga cikin mutanen da abin ya shafa sun hada kai suka kai harin ramuwar gayya, lamarin da ya sa wasu mutum hudu daga dayan bangaren suka samu raunuka.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta kashe Naira biliyan 10, Tinubu ya kafa kwamitin gaggawa a yaki Ebola

Majiyar ta ce sabanin rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta, ba harin ‘yan bindiga aka kai ba, illa rikicin da ya samo asali daga tsohuwar takaddama kan gonar.

Rahotanni sun bayyana cewa rikici kan gona ya jawo jikkatar mutane akalla 10.
Wasu manoma suna aikin shuka a gonarsu yayin da damina ta sauka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An kai wadanda suka jikkata asibiti

An bayyana cewa wasu daga cikin wadanda suka jikkata sun samu raunukan harbin bindiga, yayin da wasu suka samu munanan sara da adduna.

Ana kula da wasu daga cikin wadanda abin ya shafa a babban asibitin Rabah, yayin da aka mayar da wadanda raunukansu suka tsananta zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto.

Shugaban karamar hukumar Rabah, Hon. Yusuf Muhammad Rabah, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an samu nasarar kwantar da hankulan bangarorin biyu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai samu cikakken bayani kan lamarin ba.

Rikici kan gona ya jawo kisan sojoji

A wani labari, mun ruwaito cewa, Olorogun Sleek Oshare, wani shugaban al'umma a Delta, ya ce rikicin gona ne ya jawo aka kashe sojoji a jihar.

Akalla sojoji 17 ne aka kashe a garin Okuoma da ke jihar Delta a makon da ya gabata, lamarin da ya jawo tofin Allah-tsine daga al'ummar Najeriya.

An ruwaito cewa, an bankawa garin Okuoma wuta biyo bayan kasashe sojojin da aka yi, lamarin da ya jawo asarar dukiya da jikkata mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com