Bayan Yi Masa Ihu a Amurka, Trump Ya Fadi Lokacin Yin Nasara kan Iran
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya nuna alamun samun nasara a yakin da kasarsa ta kaddamar kan Iran kwanaki
- Donald Trump ya nuna cewa Amurka na yin nasara a yakin, inda ya bayyana lokacin da za a samu cikakkiyar nasara kan Iran
- Shugaban na Amurka ya bayyana cewa killace tashoshin jiragen ruwan Iran ya matsa mata lamba domin a kulla yarjejeniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin New York, Amurka - Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta sanar da ‘cikakkiyar nasara’ a kan Iran nan da makonni biyu.
Maganar shugaban ƙasar na Amurka na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan da Iran da Isra'ila suka amince da tsagaita mafi munin tsanantar tashe-tashen hankula a tsakaninsu tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a watan Afrilu.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa Trump ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron yakin neman zaɓe na Sanata Lindsey Graham, wani amintaccen abokin kawance na jam'iyyar Republican.
Yaushe Amurka za ta yi nasara kan Iran?
“Mun kasance tawaga da ke da tauri sosai, kuma ina tsammanin muna yin nasara a wannan yaƙin, amma lallai za a yi nasarar ne a cikin makonni biyu masu zuwa lokacin da za mu sanar da cikakkiyar nasara."
“Zai kasance cikakkiyar nasara. Zai auku nan ba da jimawa ba, kuma farashin mai zai fado ƙasa warwas.”
- Shugaba Donald Trump
Trump ya ce an matsawa Iran
Tun da farko Trump ya ce killace tashoshin ruwa na Iran da Amurka ta yi yana ƙara matsa lamba don kulla yarjejeniya
Ya bayyana cewa ba ya son ci gaba da kai hare-hare saboda mutane da dama za su rasa rayukansu, tashar AP ta kawo rahoton.
“Ina tsammanin muna … kusa sosai da samun wata yarjejeniya mai kyau, mai ƙarfi, da gagarumin tasiri."
“Idan muka tafi muka jefa bam, wanda za mu iya yin hakan cikin sauƙi idan muna so, kuma muka shafe wasu makonni biyu ko uku muna jefa bama-bamai, ba zai rage musu komai ba baki ɗaya, amma kuma ba za a samu mashigar Hormuz a buɗe ba har tsawon watanni."
“Idan muka jefa bama-baman, kun san za a kashe mutane da dama. Wane ne yake son yin hakan? Ni ba na so, kuma … za mu samu takardar yarjejeniya da aka sanya wa hannu wadda a gaskiya ta fi ƙarfin jefa bama-baman."
“Abin da ya nuna cewa yana da gagarumin tasiri shi ne killacewar. Killacewar ta kasance tana da ƙarfi fiye da jefa bama-bamai, kuma a gaskiya ya kasance haɗakar farmakinmu na farko sannan kuma da killacewar, amma kun san tattalin arzikinsu yana fuskantar matsi sosai, kuma za su kulla yarjejeniya.
- Shugaba Donald Trump

Source: Getty Images
An yi wa Trump ihu a Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya fuskanci ihu a wajen wani wasan kwallon kwando.
An yi wa Shugaba Trump ihun ne kafin a fara wasan ƙarshe na gasar kwallon kwando ta NBA a babban filin wasa na Madison Square Garden da ke birnin New York.
Ihun dai ya gudana ne lokacin da aka nuna hoton Trump a jikin babban allon da ke filin wasan yayin da ake rera taken kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

