Bayan Tinubu Ya Rantsar da Shi, Sabon Ministan Lantarki Ya Fara da Bai wa Yan Najeriya Hakuri
- Sabon Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya ce ba za a iya magance matsalar wutar lantarkin Najeriya cikin gaggawa ba
- Ya bayyana cewa matsalolin bangaren wuta sun dade suna taruwa tsawon shekaru, yana mai cewa za a warware su a hankali a hankali
- Tegbe ya bukaci yan Najeriya su kara hakuri game da rashin samun wadatacciyar wutar lantarki, ya jaddada cewa hakan zai zama tarihi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Sabon Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya bukaci 'yan Najeriya su kara hakuri kan matsalar rashin isasshiyar wutar lantarki a kasar nan.
Tegbe ya ce ba za a samu sauyi cikin kankanin lokaci ba saboda matsalolin da suka dade suna addabar bangaren lantarki, amma za a shawo kansu a hankali a hankali.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Tegbe ya bayyana hakan ne bayan rantsar da shi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan
Atiku ya yi murna da ceto mutane 360, ya ce sojoji za su iya murkushe ta'addanci a Najeriya
Yadda za a magance matsalar wutar lantarki
A cewarsa, matsalolin da suka hana bangaren lantarki motsi sun samo asali ne tun shekaru da dama da suka gabata, don haka ba za a iya warware su cikin makonni ko watanni kadan ba.
Ya ce Gwamnatin tarayya na aiwatar da sauye-sauye a bangarorin samar da wuta, isar da ita da kuma rarraba ta, domin tabbatar da ingantaccen aiki a gaba.
"Kalubalen da suka janyo bangaren wutar lantarki ya kasa kaiwa matsayin da ake bukata sun dade suna taruwa tsawon shekaru. Ba za a iya kawar da su gaba daya cikin makonni ko watanni ba," in ji shi.
Gyare-gyaren da gwamnati ke yi
Ministan ya bayyana cewa tun bayan amincewar Majalisar Dattawa da nadinsa, ya gana da hukumomi da kamfanonin da ke aikin wutar lantarki domin samar da sababbin dabarun gyara bangaren.
Ya ce an samu goyon baya daga hukumomin cikin gida da kuma kungiyoyin raya kasa na duniya da suka nuna aniyarsu ta tallafawa bangaren lantarki da kudade.

Kara karanta wannan
Matsalar tsaro: NLC da TUC sun yi barazanar hana ma'aikata zuwa wurin aiki a Najeriya
Nasarorin da aka samu a bangaren wuta
Tegbe ya ce daga cikin nasarorin farko da aka samu akwai dawo da aikin tashar samar da wutar lantarki ta Alaoji mai karfin megawatt 450 a jihar Abia, wadda ta shafe shekaru uku ba ta aiki.
Ya bayyana cewa yanzu ana iya tura har megawatt 375 daga tashar zuwa babbar hanyar rarraba wutar lantarki ta kasa, kamar yadda Premium Times ta kawo.

Source: Instagram
Haka kuma, ya ce Kamfanin Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya kaddamar da sababbin kayan aiki a Abuja da jihohin Oyo da Ogun domin karfafa isar da wuta.
Sai dai ya bukaci jama'a su kara hakuri yayin da gyare-gyaren ke ci gaba da samar da sakamako mai kyau.
"Ba zan yi alkawarin abin da ba zan iya cika wa ba, amma zan tabbatar da cewa za ku ci gaba da ganin sauye-sauye a bangaren wutar lantarki. Za mu ci gaba da aiki," in ji shi.

Kara karanta wannan
"Ku daina yi wa Fulani kudin goro," Peter Obi ya yi jan hankali kan ayyukan 'yan bindiga
Dangote zai zuba jari a lantarki
A wani labarin, kun ji cewa shugaban rukunin kanfanonin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote ya shirya zuba jari mai girma a fannin samar da wutar lantarki.
Aliko Dangote na shirin samar da megawatt 20,000 na wutar lantarki, wanda ake ganin zai yaye duk wata matsalar karancin wuta a Najeriya.
Dangote ya kuma lissafo wasu manyan ayyukan da kamfaninsa ke yi, ciki har da samar da takin zamani, iskar gas (LNG), da gina tashar jirgin ruwa mai zurfi.
Asali: Legit.ng