An Samu Matsala, Mutum 3 Sun Mutu a Gidan Gwammatin Jihar Neja

An Samu Matsala, Mutum 3 Sun Mutu a Gidan Gwammatin Jihar Neja

  • Akalla mutane uku sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon turmutsitsi a Gidan Gwamnatin Jihar Neja
  • Rahotanni sun nuna cewa wata mace da ’yarta da ke zaune a matsayin ’yan gudun hijira na cikin wadanda suka mutu
  • Lamarin ya faru ne bayan matasa sun taru a Gidan Gwamnati kan zanga-zangar mutuwar masu hakar ma’adinai 37 a hannun NSCDC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Akalla mutane uku sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon turmutsitsi a gidan gwamnatin jihar Neja da ke Minna.

A halin yanzu, ana kula da wadanda suka jikkata a Babban Asibitin Minna, inda aka ce lamarin ya faru ne a daren ranar Talata.

Neja.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago da wasu matasa Hoto: Umaru Mohammed Bago
Source: Facebook

Daily Trust ta ce lamarin da ya faru ne lokacin da aka gayyaci wasu matasa da ake zargin suna da alaka da shirin zanga-zanga kan mutuwar masu hakar ma’adinai 37 domin su janye shirinsu.

Kara karanta wannan

Akwai alheri: An buɗe shirin da ake buƙatar matasa 'yan shekaru 15 zuwa 35 su cike a Najeriya

Mutum 3 sun mutu a gidan gwamnatin Neja

Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai wata mata mai suna Dije da ’yarta, Hurairat, wadanda dukkaninsu ’yan gudun hijira ne daga kauyen Allawa da ke Karamar Hukumar Shiroro.

An ruwaito cewa mijin Hurairat, Abubakar, wanda mahauci ne, ’yan bindiga sun kashe shi a shekarar 2023 a kan hanyar Allawa zuwa Pandogari.

Bayan harin da kuma barin al’ummar Allawa sakamakon lamarin, Hurairat ta koma Minna inda ta zauna a matsayin ’yar gudun hijira.

Dije, wadda take zaune tare da mijinta a matsayin ’yar gudun hijira a Gurmana, ta je wajen ’yarta Hurairat. A lokacin ne suka ji cewa gwamnan zai raba kudi a Gidan Gwamnati, sannan suka nufi wurin.

Mallam Musa Allawa, daya daga cikin ’yan gudun hijirar, ya shaida cewa za a yi jana’izar Dije da Hurairat da karfe 10 na safe ranar Laraba.

Me ya haddasa turmutsitsi a Minna?

Kara karanta wannan

'Yan daba sun sassara matashi mai shayi da wukake har ya mutu

Wasu majiyoyi, ciki har da wasu jami’an da gwamnan ya nada, sun wallafa a kafafen sada zumunta kafin turmutsitsin cewa matasan sun taru a Gidan Gwamnati ne domin nuna goyon baya ga Gwamna Mohammed Umaru Bago.

Daya daga cikin jami’an ya bayyana cewa daga bisani wasu mutane, ciki har da mata, sun yi ta tururuwa zuwa gidan gwamnati bayan sun ji cewa gwamnan zai raba N10,000 ga wadanda suka taru.

Bago.
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago a fadar gwamnatinsa da ke Minna Hoto: Umaru Mohammed Bago
Source: Twitter

Da aka tuntubi Babban Sakataren Yada Labarai na gwamnan jihar Neja, Bologi Ibrahim, ya ce gwamnati za ta fitar da sanarwa nan gaba.

Haka kuma, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya yi alkawarin sanar dda bayanin abin da ya faru bayan kammala tattara bayanai.

Gwamna Bago na biyan albashin N500k

Kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ce gonarsa tana biyan ma’aikatan da suka kammala jami’a mafi karancin N500,000 duk wata.

Bago, wanafa ake kira da manomin gwamna, ya bayyana yadda harkar noma, musamman kiwon dabbobi, za ta iya zama babbar hanyar samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262