An Kashe 'Yan Bindiga bayan Kwamishinan 'Yan Sanda Ya Je Fagen Daga a Abuja
- Jami'an rundunar 'yan sanda sun samu nasara bayan sun yi arangama da wasu tsagerun 'yan bindiga a babban birnin tarayya Abuja
- Kwamishinan 'yan sanda na Abuja, Ahmed Mohammed Sanusi, da kansa ya jagoranci tawagar da ta fafata da 'yan bindigan a cikin daji
- Bayan hallaka wasu daga cikin 'yan bindigar, 'yan sandan sun kwato makamai tare da ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wasu jami'an rundunar 'yan sanda sun samu nasarar hallaka wasu 'yan bindiga a babban birnin tarayya Abuja.
Aƙalla mambobi biyu na ƙungiyar 'yan bindiga ne ke addabar mazauna babban birnin tarayya Abuja, 'yan sanda suka harbe har lahira.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa kwamishinan 'yan sanda na FCT, CP Ahmed Mohammed Sanusi, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a hedkwatar rundunar ranar Laraba, 10 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan
An shiga firgici da 'yan bindiga suka kai hari a Sokoto, an kashe jami'in tsaro da sace mutane
Kwamishinan 'yan sanda ya jagoranci karo da 'yan bindiga
Ahmed Mohammed Sanusi ya ce shi da kansa ya jagoranci aikin da ya yi sanadiyyar mutuwar tsagerun 'yan bindigan.
An bi sawun ƙungiyar ne biyo bayan sace mutane guda biyar na garin Paze da ke mazaɓar Byazhin a karamar hukumar Bwari a makon da ya gabata, jaridar The Guardian ta kawo rahoton.
A cewar kwamishinan 'yan sandan, an ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a lokacin aikin da ya haɗa da tawagar jami'an sashen yaƙi da garkuwa da mutane, sashen binciken sirri na rundunar 'yan sanda ta ƙasa (IRT), da kuma rundunar shiyyar Kubwa, tare da haɗin gwiwar mafarauta.
Yadda aka kashe 'yan bindiga a Abuja
Ya ce da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Talata, 9 ga watan Yunin 2026 ne ya jagoranci haɗaddiyar tawagar tsaron domin ƙaddamar da bincike da kuma aikin ceto a faɗin garuruwan Paze da Byazhin.
Aikin ya kai ga kama wasu mutane da ake zargi da aka gano da sunaye Icheh Mohammadu da Abubakar Usman, yayin da sauran mambobin ƙungiyar suka tsere zuwa cikin tsaunukan da ke kusa.
“Kuma a lokacin aikin, tawagar 'yan sandan ta kuma kwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu tare da jigidar harsasai, yayin da aka kama mambobin ƙungiyar guda biyu a lokacin musayar wuta."
- Ahmed Mohammed Sanusi
CP Mohammed Sanusi ya ce tuni aka tafi da mutane biyar ɗin da aka ceto zuwa wani asibiti da ke kusa domin duba lafiyarsu, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin sake haɗa su da iyalansu.

Source: Twitter
An kashe jagororin 'yan bindiga a Kaduna
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani kazamin ua barke tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga masu gaba da juna a jihar Kaduna.
Wannan fadan ya jawo sanadiyyar halllaka wasu manyan jagorori guda hudu yayin da aka raunata wani adadi mai tarin yawa na mayaka.
An dai kashe jagororin ne a lokacin wata mummunar arangama da aka yi tsakanin ƙungiyoyin 'yan bindiga masu hamayya da juna a karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
