"Suna da Amfani": Jagoran NDC Ya Fadi Makomar Kwankwasiyya da Obidients a Jam'iyyar

"Suna da Amfani": Jagoran NDC Ya Fadi Makomar Kwankwasiyya da Obidients a Jam'iyyar

  • Jagoran NDC na kasa, Seriake Dickson, ya gana da madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar
  • Sanata Seriake Dickson ya nuna cewa ya gana da jiga-jigan ne domin dinke barakar da ta taso a jam'iyyar mai adawa a Najeriya
  • Jagoran na NDC ya bayyana cewa kungiyoyin Kwankwasiyya da Obidients suna da rawar da za su taka a cikin sabuwar jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jagoran NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson, ya bayyana cewa yana kokarin gyara saɓani a tsakanin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar.

Sanata Seriake Dickson ya bayyana hakan ne biyo bayan wani taro da ya yi da Rabiu Musa Kwankwaso da sauran manyan jiga-jigan jam'iyyar NDC.

Kwankwaso ya gana da jagoran NDC na kasa
Sanata Seriake Dickson da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bayan sun gana a Abuja Hoto: @iamHSDickson
Source: Twitter

Dickson ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na X bayan ya karɓi baƙuncin Kwankwaso da mambobin shugabancin jam'iyyar a gidansa ranar Talata, 9 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

NNPP ta zargi Kwankwaso da yi mata kamun kazar kuku, ta mika bukata ga INEC

Seriake Dickson ya gana da Rabiu Kwankwaso

A cikin sanarwarsa, Dickson ya ce taron wani ɓangare ne na shirin tattaunawa da ake ci gaba da yi da nufin tabbatar da jituwa tsakanin shugabannin jam'iyyar a Kano da kuma jagoran jam'iyyar na jihar, wanda kuma shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC.

Tsohon gwamnan na jihar Bayelsa ya ce saurin fitowar NDC a matsayin babbar jam'iyyar hamayya ya haifar da saɓani da kuma buri mabanbanta na neman fada a tsakanin mambobi, wanda hakan abu ne da ba za a iya kauce masa ba.

NDC na son warware rikice-rikicen gida

Sai dai, ya ce ana magance irin waɗannan ƙalubale ta hanyar tattaunawa, tuntuɓa, da kuma ba juna hakuri

“NDC ta yi gaggawar zama a matsayin babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, kuma kamar kowace tafiyar siyasa da ke haɓaka, saɓani da arangamar buƙatu abubuwa ne da ba za a iya kauce masu ba."

Kara karanta wannan

Rikicin NDC: Abin da Kwankwaso da Seriake Dickson suka tattauna a zaman Abuja

- Sanata Seriake Dickson

Jam'iyyar NDC ba ta nuna fin karfi

Dickson ya yi watsi da iƙirarin nuna fin karfi wajen zabar 'yan takara a cikin jam'iyyar, inda ya jaddada cewa NDC ta kasance tana ba da dama ga tsarin dimokuraɗiyya domin ayyana 'yan takararta a faɗin jihohi.

Ya ƙara da cewa tattaunawar da aka yi da Kwankwaso da sauran masu ruwa da tsaki ta haifar da ɗa mai ido, kuma ya nuna kwarin gwiwar cewa dukkan ɓangarorin za su ci gaba da aiki tare domin cimma muradun zaɓe na jam'iyyar.

Dickson na kokarin sulhunta 'yan NDC
Seriake Dickson na gaisawa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bayan sun gana a Abuja Hoto: @iamHSDickson
Source: Twitter

Ya batun 'yan Kwankwasiyya da Obidients?

Jagoran na NDC ya bayyana ƙungiyoyin magoya baya na Kwankwasiyya da Obidient a matsayin muhimman rukunoni waɗanda za a haɗa mambobinsu cikin tsarin jam'iyyar a faɗin ƙasar.

Ya ce tun da farko ya karɓi wata tawaga daga ƙungiyar Obidient Movement kuma ya tabbatar musu da sanya su cikin ayyukan jam'iyyar a matakai mabanbanta.

Dickson ya ce za a faɗaɗa irin wannan tsari zuwa ga ƙungiyar Kwankwasiyya Movement da zarar an mika jjerin sunayen jagororinta ga jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Gawuna na shirin komawa ADC daga NDC, ya mika bukatunsa ga jam'iyyar

NNPP ta yi zargi kan Kwankwaso

A wani labarin kuma, jam'iyyar NNPP ta yi zargi kan madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya yi mata takara a zaben 2023.

NNPP ta zargi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ci gaba da shiga harkokin jam’iyyar duk da cewa ya yanke alaka da ita zuwa sabuwar jam'iyya.

Ta bayyana cewa Kwankwaso na ci gaba da yin tasiri a cikin jam’iyyar ta hannun wasu magoya bayansa da ake zargin ya bari a cikinta bayan ficewarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng