Gwamna Abba Ya Kafa Tarihi, Ya Yi Aikin da Kwankwaso, Ganduje da Shekarau Suka Gaza a Kano

Gwamna Abba Ya Kafa Tarihi, Ya Yi Aikin da Kwankwaso, Ganduje da Shekarau Suka Gaza a Kano

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gyara tare da dawo da aikin wurin rarraba ruwa daga madatsar Goron Dutse
  • Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Abba ya yi nasarar dawo da wurin aiki bayan sama da shekaru 30 da aka yi watsi da shi
  • Gwamnan ya ce dawo da wurin aiki na daga cikin manyan kokarin gwamnatinsa na farfado da muhimman ababen more rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da madatsar ruwa ta Goron Dutse, bayan sama da shekaru 30 da wurin ya daina aiki.

Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya bayan bikin da aka gudanar a Kano.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fitar da sanarwa, ya hana bikin ranar samun 'yancin kan Najeriya

Abba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a wurin taro Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A cewar Hashim kamar yadda Leadership ta ruwaito, wannan ci gaba wani muhimmin mataki ne wajen inganta ingancin samar da ruwan sha na gwamnati a fadin birnin Kano.

Abba ya gyara madatsar Goron Dutse

Ya bayyana cewa a yanzu ana tura ruwa daga Kamfanin Tace Ruwa na Challawa zuwa madatsun Goron Dutse domin rarrabawa ga al’umma.

A wajen bikin, Abba ya bayyana farfado da madatsar ruwan a matsayin wani gagarumin tarihi ga jihar da kuma muhimmin mataki ga mazauna Kano da suka shafe tsawon lokaci suna fuskantar matsalolin samun ruwan sha.

“Wannan aiki ne na tarihi ga Jihar Kano. An bar madatsar Goron Dutse sama da shekaru 30 ba ta aiki, kuma yau mun dawo da ita aiki domin ta yi wa al’ummar Kano hidima,” in ji Abba.

Gwamnan ya ce dawo da wurin aiki na daga cikin manyan kokarin gwamnatinsa na farfado da muhimman ababen more rayuwa da kuma magance matsalolin da suka dade suna addabar mazauna jihar.

Kara karanta wannan

Atiku ya ragargaji Tinubu kan karbo bashin kusan Naira tiriliyan 2

Ya ƙara da cewa fara rarraba ruwa daga Goron Dutse zai taimaka wajen inganta samun ruwan sha a fadin birnin Kano, yayin da ya sake tabbatar da kudirin gwamnatinsa na kammala sauran muhimman ayyukan ruwa a fadin Kano.

Adadin ruwan da madatsar ke dauka

Hashim ya bayyana cewa madatsar Goron Dutse na da karfin ajiya na kusan lita miliyan 39.8, wanda ya kunshi madatsu uku masu daukar lita miliyan 10, miliyan 7.3 da miliyan 22.5.

Kwamishinan ya yaba wa Gwamna Abba bisa bai wa farfado da wurin, yana mai cewa goyon bayan siyasa da na gudanarwa da gwamnatin ta bayar ya taka muhimmiyar rawa wajen dawo da madatsar aiki.

Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Bayanai sun nuna cewa aikin wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 11, kamfanin China Civil Engineering Construction Corporation (CCECC) ne ya gudanar da shi.

Gwamna Abba ya jinjinawa Tinubu

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yaba wa Shugaba Tinubu kan kafa Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND).

Gwamna Abba ya bayyana cewa shirin wani muhimmin mataki ne da zai iya faɗaɗa damar samun ilimin manyan makarantu a Najeriya.

Ya ce NELFUND zai samar wa ɗalibai da iyayensu ƙarin damar biyan kuɗin manyan makarantu tare da rage matsalolin kuɗi da ke hana wasu samun ilimi a matakin gaba da sakandare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262