Mutuwa Ta Sake Girgiza Najeriya, Sarkin Gazargamu Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Masar
- Sarkin Gazargamu na jihar Yobe, Mai Martaba Alhaji Ahmad Tijjani Ibn Saleh, ya rasu bayan ya shafe lokaci yana fama da rashin lafiya
- Rahotannni sun tabbatar da cewa sarkin ya rasu ne a birnin Alkahira na ƙasar Masar inda yake karɓar magani a wani asibiti
- Iyalan marigayin sun bayyana cewa rayuwar marigayi Ahmad Tijjani ta kasance cike da hikima, tawali’u da hidimar al’umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Yobe, Nigeria - An shiga jimami a masarautar Gazargamu da ke jihar Yobe bayan samun labarin rasuwar sarkin masarautar, Mai Martaba Alhaji Ahmad Tijjani Ibn Saleh.
Rahotanni sun nuna cewa Sarkin ya rasu ne a ranar Talata, 9 ga watan Yuni, 2026 a birnin Alkahira na ƙasar Masar, inda yake jinya sakamakon doguwar rashin lafiya da ya yi fama da ita.

Source: Facebook
An sanar da rasuwar Sarkin Gazargamu
Daily Trust ta ruwaito cewa dan marigayin, Injiniya Tijjani Hamisu Bala, wanda shi ne Shugaban Hukumar Kula da Gyaran Hanyoyi ta Jihar Yobe (YORMA), ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa.
A cikin sanarwar da ya fitar, Tijjani Hamisu ya bayyana marigayin a matsayin uba, jagora kuma sarki wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’ummarsa da bil’adama hidima.
Ya ce
"Cikin jimami da mika wuya ga ƙaddarar Allah SWT mjke sanar da rasuwar mahaifinsa, Mai Martaba Alhaji Ahmad Tijjani Ibn Saleh, Sarkin Gazargamu, wanda ya koma ga Mahaliccinsa a yau 9 ga watan Yuni, 2026 bayan doguwar jinya.
An yaba da nagartar marigayin
A cewar Tijjani, rayuwar marigayin ta kasance cike da hikima, tawali’u, jarumtaka da kuma sadaukarwa wajen yi wa jama’arsa hidima, kama yadda NTA News ta wallafa.
Ya ce kyakkyawan shugabanci, kulawa da irin gudunmawar da basaraken ya bayar za su ci gaba da kasancewa abin koyi ga iyalansa da al’ummar masarautar baki ɗaya.

Kara karanta wannan
Daga zuwa wurin taro, shugaban kungiyar kwadago a Najeriya ya rasu a kasar Switzerland
Haka kuma ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya sanya shi a Aljannatul Firdausi, sannan Ya ba iyalansa da al’ummar masarautar Gazargamu juriyar jure wannan babban rashi.
Yushe za a yi jana'izar Sarkin?
Har zuwa lokacin da ake tattara wannan rahoto, ba a bayyana lokacin da za a yi jana’izar marigayin ba.
Haka kuma ba a tabbatar da ko za a dawo da gawarsa Najeriya domin binne shi ko kuma za a yi jana’izarsa a ƙasar Masar ba.

Source: Original
Rasuwar Sarkin Gazargamu ta jefa al’ummar masarautar da ma jihar Yobe cikin jimami, yayin da ake ci gaba da karɓar saƙonnin ta’aziyya daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Malam Abubakar Pharmacy ya rasu
A wani rahoton, kun ji cewa matashin malamin addinin musulunci a jihar Gombe, Malam Abbakar Sadiq Pharmacy ya riga mu gidan gaskiya.
Tsohon ministan sadarwa kuma 'dan takarar gwamnan Gombe a inuwar PDP, Farfesa Isa Pantami ya tabbatar da rasuwar Malam Abbakar.
Wani 'dan unguwar Pantami, Abubakar Ibrahim ya shaidawa Legit Hausa cewa marigayin ya sha fama da jinya tun a nan Gombe, kafin daga bisani a tafi da shi zuwa Kano.
Asali: Legit.ng
