Ana Shirin Zaben 2027, Jam'iyyar ADC Ta Su Atiku Ta Gamu da Babban Koma Baya
- Wasu ’yan takarar Majalisar Dokokin Jiha na ADC daga jihohin Zamfara, Plateau, Taraba da Jigawa sun sanar da komawa jam’iyyar APC
- ’Yan siyasar sun bayyana goyon bayansu ga ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027
- Shugaban APC, Nentawe Yilwatda, ya ce jam’iyyar za ta bai wa waɗanda suka sauya sheka damar taka rawa wajen ci gabanta da kasa baki daya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wasu ’yan takarar kujerun Majalisar Dokokin Jiha na jam’iyyar ADC daga jihohin Zamfara, Plateau, Taraba da Jigawa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
’Yan siyasar sun bayyana matakin ne a ranar Litinin, 28 ga watan Satumban 2026 yayin da suka kai ziyara hedikwatar jam’iyyar APC ta ƙasa da ke Abuja.

Source: Twitter
Abimbola Tooki, mai ba shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, shawara ta musamman, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a shafin X.
’Yan siyasar sun bayyana goyon bayan Tinubu
A cewar sanarwar, waɗanda suka sauya sheka sun kuma bayyana goyon bayansu ga ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na sake neman kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Aslam Gambiyar, wanda ya jagoranci tawagar, ya ce sun gamsu “ba tare da wata shakka ba” cewa Tinubu ne ɗan takarar da zai iya kai Najeriya zuwa wani matsayi mafi girma.
Gambiyar ya ce wannan dalilin ne ya sa suka yanke shawarar ficewa daga ADC tare da shiga APC domin mara wa Tinubu baya a ƙoƙarinsa na sake lashe zaɓen.
Yilwatda ya karɓi waɗanda suka sauya sheka
Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya yaba wa waɗanda suka sauya sheka saboda, a cewarsa, sun fifita muradun ƙasa fiye da burinsu na siyasa.
“Matasa ne ke shiga sahunmu na masu son ci gaba. Ina farin ciki da kuka yi murabus kuma kuka miƙa takardun murabus ɗinku ga rassan jam’iyyarku."
“Abin da ya rage yanzu shi ne ku koma mazabunku ku fara aiki,” in ji Yilwatda.
Ya ce matakin da ’yan siyasar suka ɗauka na ajiye burinsu na kashin kansu domin mara wa abin da suka bayyana a matsayin babbar manufar ƙasa baya abin a yaba ne.
Ya ƙara da cewa APC za ta samar musu da damar bayar da gudunmawa mai ma’ana ga jam’iyyar da kuma ƙasar.
Yilwatda ya kare ayyukan gwamnatin Tinubu
Yilwatda ya yi watsi da ikirarin cewa Shugaba Tinubu bai damu da Arewa ba, yana mai cewa girman ayyukan more rayuwa da ake gudanarwa a yankin ya nuna akasin hakan.
Ya ambaci aikin hanyar Abuja–Kano–Maiduguri mai tsawon kilomita 1,000, hanyar gabar teku, da hanyoyin Jos–Akwanga, Kwara–Niger, Sokoto–Kebbi, Laila–Sokoto da Kano–Daura a matsayin manyan ayyukan da gwamnatin Tinubu ke gudanarwa.

Source: Twitter
Batun shari'ar jam'iyyar ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, mai shari’a Peter Lifu ya dage sauraron babbar shari’a da wani jigo a jam’iyyar ADC, Nafiu Bala, ya shigar kan shugabancin jam’iyyar zuwa ranar 5 ga Oktoban 2026.
Shari’ar ta ƙunshi kalubalen da ake yi wa shugabancin jam’iyyar karkashin Sanata David Mark da Rauf Aregbesola da sauran mambobin kwamitin gudanarwa na wucin gadi.
Asali: Legit.ng

