Dalibai Sun Fara Gudun Neman Tsira da Wani Malami Ya Yi Shigar 'Yan Bindiga a Makaranta

Dalibai Sun Fara Gudun Neman Tsira da Wani Malami Ya Yi Shigar 'Yan Bindiga a Makaranta

  • An shiga yanayin tashin hankali da rudani a wata makaranta da ke jihar Legas bayan dalibai sun yi zaton ‘yan bindiga ne suka kai hari
  • Rahotanni sun nuna cewa wani malami ne ya sanya kayan da suka yi kama da na ‘dan bindiga domin darasin fadakarwa da aka shirya
  • Dalibai, malamai da iyaye sun shiga firgici suna gudun ceton rai amma daga baya an gano cewa wasan kwaikwayo ne kawai domin ilmantarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Wani yanayi na rudani da firgici ya mamaye wata makaranta a jihar Legas bayan wani malami ya yi shigar da ta sa dalibai suka yi zaton ‘yan bindiga ne suka kai hari.

Lamarin ya faru ne a makarantar Ijaiye Ojokoro Junior College da ke kan titin Tigbetigbe a yankin Ojokoro na jihar Legas ranar Laraba da safe.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 6 sun mutu yayin da suka yi yunkurin kai hari a jihar Zamfara

Legas.
Taswirar jihar Legas da ke Kudu maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yadda lamarin ya faru a Legas

Rahoton vanguard ya nuna cewa kamar yadda aka saba gudanar da shirin fadakarwa na mako-mako a makarantun jihar Legas, an ware wannan rana domin tattaunawa kan matsalar ‘yan bindiga.

Domin sa darasin ya fi daukar hankali, wani malami ya yanke shawarar sanya kayan da suka yi kama da na ‘yan bindiga domin nuna wa dalibai yadda irin wadannan masu laifi suke.

Sai dai da malamin ya fito daga motarsa yana nufar filin taron makarantar, dalibai suka dauka cewa ainihin ‘dan bindiga ne ya shigo makarantar.

Dalibai da malamai sun rika gudu

Wani ganau ya bayyana cewa nan take dalibai suka fara gudu cikin tsoro suna ihu da cewa, “‘yan bindiga! ‘yan bindiga!

Yayin da daliban sauran makarantu uku da ke cikin harabar makarantar guda suka ji ihun, su ma suka fara gudu domin tsira.

Ba dalibai kadai ba, wasu malamai ma sun shiga cikin firgici inda suka rika neman mafaka, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kashe babban soja da wasu sojoji 7 a Kaduna

Iyaye sun garzaya zuwa makaranta

Lamarin ya haddasa firgici a unguwar baki daya, yayin da iyaye suka yi gaggawar zuwa makarantar domin daukar ‘ya’yansu bayan samun labarin cewa wai ‘yan bindiga sun kai hari.

Wani mazaunin yankin ya ce ya fito motsa jiki da safe ne lokacin da ya ga dalibai suna gudu cikin tashin hankali.

“Na tambaye su abin da ya faru, sai suka ce ‘yan bindiga sun shiga makaranta suna kashe mutane,” in ji shi.
Gwamna Sanwo-Olu.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu a fadar gwamnatinsa da ke Ikeja Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Source: Facebook

Ya kara da cewa bayan isa makarantar, daya daga cikin shugabannin makarantar ya bayyana masa cewa wasan kwaikwayo ne kawai ya haddasa rudanin.

An ce tituna da wuraren da ke kusa da makarantar sun cika da jama'a masu neman sanin hakikanin abin da ke faruwa kafin daga bisani a gano cewa babu wani hari da aka kai.

Halin da ke ciki kan sace daliban Oyo

A baya, kun ji cewa 'yan bindigar da suka sace dalibai a makarantu uku a jihar Oyo sun gindaya sharudda hudu kafin sako duka mutanen da ke hannunsu.

Kara karanta wannan

Yadda yan bindiga suka harbe wani dattijo bayan sace mutum 39 a Zamfara

Daga cikin sharuddan da yan ta'addan suka kafa har da sakin wasu shugabanninsu da ake tsare da su da kuma biyan kudin fansa.

Gwamnatin Oyo ta ce ba za ta yi tsokaci kan sharuɗɗan ko yadda ake tattaunawa ba domin hakan na iya kawo cikas a kokarin ceto daliban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262