An Shiga Firgici da 'Yan Bindiga Suka Kai Hari a Sokoto, an Kashe Jami'in Tsaro da Sace Mutane
- 'Yan bindiga sun yi aika-aika bayan sake kai harin ta'addanci a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
- Tsagerun 'yan bindigan sun kashe jami'in tsaro tare da sace mutane masu yawa wadanda ba a san adadinsu ba
- 'Yan bindigan sun kai harin ne da daddare lokacin da mafi yawan mutane ke gidajensu domin samun hutu kafin gari ya waye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Wani jami'in rundunar tsaro ta al'umma ta jihar Sokoto ya rasa ransa a wani harin 'yan bindiga.
'Yan bindigan sun kuma sace mutane da dama lokacin da suka farmaki garin Sabon Birni da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa 'yan bindigan sun kai harin ne a daren ranar Litinin, 8 ga watan Yunin 2026.
'Yan bindiga sun kai hari a Sokoto
Majiyoyi mabanbanta sun tabbatar da aukuwar lamarin, inda suka bayyana shi a matsayin yunƙuri na baya-bayan nan da 'yan bindiga suka yi na shiga cikin garin.
Garin dai a halin yanzu yana karɓar bakuncin mutane da dama da suka rabu da muhallansu daga garuruwan da ke maƙwabtaka da shi waɗanda rashin tsaro ya shafa.
Mamban da ke wakiltar mazaɓar Sabon Birni a Majalisar dokoki ta jihar Sokoto, Hon. Aminu Boza, ya tabbatar da harin, inda ya bayyana cewa maharan sun tafi da mutane da dama.
Mutane nawa aka sace?
Sai dai, Aminu Boza ya lura cewa ba za a iya tabbatar da takamaiman adadin mutanen da aka sace ɗin ba tukuna.
“Ba zan iya ba da takamaiman adadin mutanen da aka sace ba saboda Sabon Birni ba ƙaramar al'umma ba ce. Wasu mazauna garin ka iya kasancewa sun gudu zuwa cikin dajin da ke kusa, yayin da wasu kuma ƙila ba sa cikin garin a lokacin da harin ya auku."

Kara karanta wannan
Babu zancen shari'ar Musulunci: Ƴan bindiga da suka sace dalibai a Oyo sun fadi bukatunsu
"Har sai an gudanar da bincike mai zurfi, zai kasance da wahala a iya tabbatar da takamaiman adadin."
- Aminu Boza
'Yan bindiga na yawan yunkurin kawo hari
Wani mazaunin garin, wanda ya yi magana da sharaɗin sakaya sunansa, ya yi iƙirarin cewa an sace kusan mutane 10 a lokacin harin.
“Wannan shi ne yunƙuri na uku da 'yan bindiga suka yi na mamaye Sabon Birni, kuma sun yi amfani da hanya guda da suka yi amfani da ita a hare-haren baya."
"Sun kashe jami'in tsaro na al'umma guda ɗaya kuma sun sace kusan mutane 10." Inji majiyar
Aminu Boza ya bayyana cewa harin ya auku ne a Kantin Gabas, wanda ke can bayan gari a gefen garin Sabon Birni kusa da filin sallar Idi na al'ummar garin.
“Ba za mu iya cewa harin bai auku a Sabon Birni ba saboda wurin yana daidai wajen garin ne kuma shi ne filinmu na sallar Idi."
- Aminu Boza
A cewar ɗan majalisar, jami'in tsaron al'ummar da aka kashe ya samu raunin harbin bindiga ne a hannunsa a lokacin harin, kuma daga bisani ya rasu yayin da ake tafiya da shi zuwa asibiti a safiyar ranar Talata, 9 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Borno ta yi maganar biyan Boko Haram kudin fansa kafin a ceto mutane 360

Source: Original
Wane bayani 'yan sanda suka yi?
Legit Hausa ta tuntubi mai magana da yawun bakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa’i, domin samun karin bayani kan harin.
DSP Ahmad Rufai ya ce har yanzu bai samu cikakkun bayanai kan lamarin ba amma ya yi alkawarin tuntuɓar DPO mai kula da yankin domin samun ƙarin bayani.
"Ina ta kokarin tuntubar DPO na yankin domin samun karin bayani, ka san da yake yankin suna da matsalar sabis"
- DSP Ahmad Rufai
'Yan sanda sun fafata da 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa jami'anta sun fafata da wasu 'yan bindiga.
Rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa ta samu nasarar kashe wasu ‘yan bindiga uku a wani farmaki da ta kai cikin dajin Jangebe.
An gudanar da aikin ne bayan tura motocin sulke (APCs) da kuma motocin CSK da Gwamnatin jihar Zamfara ta samar domin inganta ayyukan sintiri.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
