Daga zuwa Wurin Taro, Shugaban Kungiyar Kwadago a Najeriya Ya Rasu a Kasar Switzerland
- Domingo Michael Adeleke, shugaban kungiyar kwadago t JNC reshen jihar Legas, ya rasu a Geneva bayan gajeruwar rashin lafiya
- Ya kasance cikin tawagar Najeriya a taron ƙwadago na duniya karo na 114, wanda ke ci gaba da gudana a Geneva da da ke Switzerland
- Kungiyar NLC ta bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga harkar ƙwadago da kare haƙƙin ma’aikata a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Geneva, Switzerland - Tawagar Najeriya da ke halartar taron kwadago na duniya (ILC) karo na 114 a birnin Geneva na ƙasar Switzerland ta shiga jimami bayan rasuwar fitaccen jagoran ƙwadago, Domingo Michael Adeleke.
Adeleke, wanda shi ne shugaban kungiyar kwadago ta JNC na jihar Legas, ya rasu ne ranar Talata bayan gajeruwar rashin lafiya yayin da yake halartar taron a matsayin ɗaya daga cikin wakilan Najeriya.

Source: UGC
Yadda Adeleke ya rasu a Geneva
Rahotannin da Vanguard ta tattaro sun nuna cewa marigayin ya fara fama da rashin lafiya ne a lokacin taron, inda aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawar likitoci.
Sai dai duk da ƙoƙarin da aka yi domin ceton rayuwarsa, ya rasu bayan wani ɗan lokaci a asibiti.
Ƙungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta tabbatar da rasuwar tasa, tana mai bayyana shi a matsayin jajirtaccen ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ma’aikata da walwalarsu.
A cewar wata sanarwa daga jami’in NLC, rasuwar Adeleke babban rashi ne ga ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya.
Gudunmawar Adeleke ga ma’aikata
Marigayin memba ne na kungiyar ma'aikatan gwamnati ta Najeriya (NCSU) kuma ya yi fice wajen fafutukar inganta rayuwar ma’aikata da kare muradunsu.
A matsayinsa na shugaban JNC na Legas, ya taka muhimmiyar rawa wajen tattaunawa da gwamnati kan albashi, walwala da sauran haƙƙoƙin ma’aikata.
NLC ta ce Adeleke ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da adalci, ingantaccen aiki da kuma kare muradun ma’aikata a matakai daban-daban.
NLC ta fara shirin dawo da gawarsa
Shugabannin NLC sun kai ziyara asibitin da aka ajiye gawarsa domin nuna alhini tare da fara shirye-shiryen dawo da gawar zuwa Najeriya.
Kungiyar ta mika ta’aziyya ga iyalansa, abokan aikinsa da kuma daukacin ‘yan ƙwadago a fadin ƙasar nan, kamar yadda PM News ta rahoto.

Source: Getty Images
NLC ta ce za a ci gaba da tunawa da Adeleke saboda gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban harkokin ƙwadago da kare haƙƙin ma’aikata.
Rasuwarsa ta girgiza mahalarta taron ILC na bana, wanda ya haɗa gwamnatoci, masu daukar ma’aikata da ƙungiyoyin ƙwadago daga sassa daban-daban na duniya domin tattauna batutuwan aiki da walwalar ma’aikata.
Yan kwadago sun taso gwamnatin Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa NLC da TUC sun yi barazanar daukar matakai masu tsauri idan ba a dakile yawaitar kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro ba.

Kara karanta wannan
Matsalar tsaro: NLC da TUC sun yi barazanar hana ma'aikata zuwa wurin aiki a Najeriya
Kungiyoyin kwadagon sun ce matsalar tsaro ta kai wani mataki mai hadari, inda ma’aikata a sassa daban-daban na kasar ke fuskantar barazanar rasa rayukansu yayin zuwa aiki.
Shugaban NLC , Joe Ajaero, da Mataimakin shugaban TUC, Oyibo Jimoh, ne suka bayyana hakan a taron yan kwadago na duniya (ILC) da ake yi a birnin Geneva da ke kasar Switzerland.
Asali: Legit.ng

