Fada Ya Barke tsakanin Kungiyoyin 'Yan Bindiga a Kaduna, an Kashe Manyan Jagorori 4
- Wasu kungiyoyin 'yan bindiga masu gaba da juna sun gwabza kazamin fada a karamar hukumar Kachia da ke jihar Kaduna
- Mummunan fadan da 'yan bindigan suka yi, ya jawo an hallaka wasu manyan jagorori yayin musayar wutar da aka yi
- Hakazalika, wasu tarin mayaka masu yawa sun samu raunuka a cikin wanda majiyoyin tsaro suka tabbatar da aukuwarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Aƙalla hatsabiban jagorororin 'yan bindiga guda huɗu, ciki har da wani fitaccen mutum da aka gano da suna Laggu, sun gamu da ajalinsu a Kaduna.
An kashe jagororin ne a lokacin wata mummunar arangama da aka yi tsakanin ƙungiyoyin 'yan bindiga masu hamayya da juna a karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
Yaushe 'yan bindiga suka yi fada?
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa lamarin ya auku ne a kewayen madatsar ruwan Rijana da ke yankin kudancin jihar, kuma lamarin ya fito fili ne biyo bayan rahotannin sirri da aka samu a ranar, Litinin, 8 ga watan Yunin 2026.
A cewar majiyoyin, arangamar ta faru ne tsakanin ɓangarorin 'yan ta'adda masu hamayya da juna da ke gudanar da ayyukansu a yankin Rijana, wani yanki da ya dade yana fuskantar ƙalubalen tsaro sakamakon ayyukan ƙungiyoyin masu aikata laifuffuka da makami.
An kashe manyan jagororin 'yan bindiga
Majiyoyin sun nuna cewa arangamar ta yi sanadin mutuwar manyan kwamandoji guda huɗu, yayin da wasu mayaka da dama suka samu raunuka masu tsanani a lokacin musayar wutar.
Kodayake ba a riga an tabbatar da takamaiman dalilin arangamar ba, amma an yi amannar cewa irin waɗannan tashe-tashen hankula galibi suna da alaƙa da takaddama kan ikon yanki, gwagwarmayar shugabanci, hanyoyin samun kuɗi, ko kuma saɓani kan raba kuɗaɗen da aka samu daga ayyukan ta'addanci.
Majiyoyi sun ƙara bayyana cewa an kwashe gawarwakin kwamandojin da aka kashe yayin arangamar domin birne su.
Har yanzu ba a riga an tabbatar da sunayen sauran hatsabiban da aka kashe ɗin ba a hukumance, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano adadin mayakan da suka ji rauni da kuma ɓangarorin da suka shiga cikin arangamar.

Source: Original
Dakaru na ci gaba da sanya ido
Dakarun tsaro sun ci gaba da sanya ido sosai kan lamarin domin dakile yiwuwar kai hare-haren ramuwar gayya da kuma amfani da duk wani bayanan sirri da ya taso daga arangamar.
Majiyoyin tsaro sun ce an tsananta ayyukan sa ido da tattara bayanan sirri a duk faɗin hanyar Rijana zuwa Kachia domin bin sawun zirga-zirgar mayakan da suka tsira da ransu, da kuma tantance tasirin da lamarin zai yi ga yanayin tsaro a yankin baki ɗaya.
'Yan bindiga sun sace mutane a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin da ya yi sanadiyyar rasuwar jami'in tsaro a Sokoto.

Kara karanta wannan
An shiga firgici da 'yan bindiga suka kai hari a Sokoto, an kashe jami'in tsaro da sace mutane
'Yan bindigan sun kuma sace mutane da dama lokacin da suka farmaki garin Sabon Birni da ke karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.
A cewar wani mazaunin garin, tsagerun 'yan bindiga sun yi awon gaba da mutane fiye da 10 yayin harin wanda suka kawo cikin dare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

