"Za Su Dandana Kudarsu"; Trump Ya Yi Sabuwar Barazana ga Iran bayan Musayar Hare Hare
- Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun yi musayar sababbin hare-hare duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tsakaninsu
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya soki Iran kan abin da ya kira jan kafar da ta yi wajen tattaunawa domin cimma yarjejeniya
- Donald Trump ya nuna cewa Iran ta rasa damar da ta samu domin kulla yarjejeniya mai kyau, domin yanzu za ta dandana kudarta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yi barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Shugaba Trump ya ce Iran ‘ta ɗauki lokaci mai tsawo’ kafin ta cimma yarjejeniya kuma yanzu za ta dandana kudarta.

Source: Getty Images
Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Laraba, 10 ga watan Yunin 2026.
Amurka da Iran sun yi musayar wuta
Tun da farko Shugaba Donald Trump ya kare hare-haren ramuwar gayya da Amurka ta kai wa Iran, inda ya siffanta martanin sojan a matsayin mataki na dole biyo bayan kakkabo jirgin helikofta na rundunar sojan kasa ta Amurka.
Rahoton BBC ya nuna cewa an ƙaddamar da hare-haren ne a ranar Talata bayan an kakkabo wani jirgin helikofta ƙirar Apache a gabar tekun Oman, wani lamari da birnin Washington ya bayyana a matsayin ayyukan kare kai a kan wuraren da Iran ta farmaka.
Shugaba Trump ya ce martanin na Amurka an yi shi ne da nufin aika saƙo mai ƙarfi ga kasar Iran bayan harbo jirgin.
Kasar Iran ta mayar da martani jim kaɗan bayan harin na Amurka, inda dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) suka sanar da cewa sun harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa zuwa sansanonin Amurka da ke yankin.
Wace barazana Trump ya yi?
Trump ya sake jaddada iƙirarin cewa an wargaza dakarun sojojin Iran, kuma rundunoninsu na ruwa da na sama ba sa aiki.
Shugaban na Amurka ya kuma yi barazanar cewa Iran za ta dandana kudarta saboda jan kafar da ta yi wajen tattaunawa domin cimma yarjejeniya.
"Dakarun sojan Iran suna cikin gagarumin ruɗani baki ɗaya. Mafi yawancinsu, kamar dakarunsu na ruwa da na sama, yanzu ma ba sa wanzuwa."
"An ragargaza su baki ɗaya. Iran surutu ce kawai ba ta tabuka komai. Mugun Gabas Ta Tsakiya ya mutu!!!"
"Sun ɗauki lokaci mai tsawo kafin su yi shawarwarin yarjejeniyar da za ta kasance mai kyau a gare su, yanzu kuma dole ne su dandana kudarsu!!!"
- Shugaba Donald Trump

Source: Facebook
Trump ya yi maganar nasara kan Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi maganar lokacin da kasarsa za ta yi nasara kan Iran.
Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta sanar da ‘cikakkiyar nasara’ a kan Iran nan da wani dan lokaci mai zuwa.
Donald Trump ya bayyana cewa ba ya son ci gaba da kai hare-hare saboda mutane da dama za su rasa rayukansu idan har aka yi hakan.
Asali: Legit.ng

