Gawuna Na Shirin Komawa ADC daga NDC, Ya Mika Bukatunsa ga Jam'iyyar
- Alamu sun nuna akwai yiwuwar tsohon Mataimakin gwamnan jihar Kano, Dr. Nasiru Gawuna, zai sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC
- Shugaban jam'iyyar ADC na Kano, Musa Ungogo, ya ba da tabbacin cewa suna tattaunawa da dan takarar na sanatan Kano ta Tsakiya a inuwar NDC a zaben 2027
- Hakazalika, ya bayyana cewa Gawuna ne ya tuntube su inda ya gabatar da bukatun da yake son samu idan ya dawo jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna, yana shirin ficewa daga jam'iyyar NDC zuwa ADC.
Gawuna na shirin sauya shekar ne biyo bayan tattaunawa da ake ci gaba da yi tsakaninsa da jam'iyyar ADC.

Source: Twitter
Shugaban jam'iyyar ADC na jihar Kano, Musa Ungogo, ya tabbatar da hakan a cikin wata hira ta musamman da ya yi da jaridar The Punch ranar Litinin, 8 ga watan Yunin 2026.
Nasiru Gawuna ya tuntubi shugabannin ADC
Musa Ungogo ya ce Gawuna ne ya fara tattaunawar ta hanyar wasu wakilai waɗanda suka haɗu da shugabannin jam'iyyar a karshen mako.
Ungogo ya yi watsi da iƙirarin da ke yawo a shafukan sada zumunta na cewa ADC ce ke zawarcin tsohon mataimakin gwamnan, inda ya jaddada cewa Gawuna ya fara tuntubarsu ta hanyar mutanensa.
“Labarin da ake yaɗawa na cewa ADC ce ta tuntuɓi Gawuna ba gaskiya ba ne. Gawuna ne da kansa ya tuntuɓe mu. Ya aiko da tawaga domin haduwa da mu, kuma an dade ana tattaunawa tun daga lokacin."
- Musa Ungogo
A cewar shugaban na ADC, tawagar ta Gawuna ta haɗa da tsohon shugaban karamar hukumar Kumbotso, Alhaji Sagir Fanshekara, da kuma Hon. Kadawa.
Ya ce tawagar ta haɗu da shi da kuma sakataren jam'iyyar na jiha a ranar Asabar a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin tattauna sharuɗɗan shigar Gawuna cikin jam'iyyar.
Gawuna ya mika bukatunsa ga ADC
Ungogo ya bayyana cewa cikin buƙatun da ɓangaren Gawuna ya gabatar har da tikitin takarar gwamna na ADC don zaɓen shekarar 2027.
Ya ƙara da cewa tsohon ɗan takarar gwamna na APC yana kuma neman matsugunin siyasa ga wasu daga cikin magoya bayansa amintattu waɗanda ke sha'awar tsayawa takarar kujerun majalisar dokoki ta jiha da na Majalisar tarayya.
Duk da tattaunawar da ake ci gaba da yi, Musa Ungogo ya jaddada cewa ba a cimma yarjejeniya ta ƙarshe ba tukuna.
“Har yanzu ana ci gaba da shawarwari. Ba a kammala komai ba tukunna. Muna son mafita da za ta kasance mai karɓuwa ga dukkan masu ruwa da tsaki kuma za ta amfani jam'iyyar."
- Musa Ungogo

Source: Facebook
An tabbatar da tattaunawar Gawuna da ADC
Wani na kusa da Nasiru Gawuna shi ma ya tabbatar da tattaunawar, amma ya ƙi cewa uffan fiye da hakan.
“Ni ba mai magana da yawunsa ba ne, kuma ba a ba ni iko na yin magana a kan lamarin ba. Abin da zan iya tabbatarwa kawai shi ne ana ci gaba da tattaunawa." Inji majiyar

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Kwankwaso ya yi barazanar ficewa daga NDC, an ji dalilin fusatar Madugu
Kwankwaso ya magantu kan takarar Gawuna
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan takarar sanata da aka ba Nasiru Gawuna a jam'iyyar NDC.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa samun takara rabo ne, kuma sanata ba karamin mukami ba ne a tsarin siyasar Najeriya.
Madugun na Kwankwasiyya ya kara da cewa suna tare da Gawuna da Aminu Abdulsalam Gwarzo da aka ba takara cikin zaman lafiya da fahimtar juna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

