"Yanzu ne Lokacin": Atiku Ya Sake Aika Sako ga 'Yan Najeriya kan Shugaba Tinubu

"Yanzu ne Lokacin": Atiku Ya Sake Aika Sako ga 'Yan Najeriya kan Shugaba Tinubu

  • Atiku Abubakar ya ce ’yan Najeriya su yi amfani da zaɓen 2027 wajen sauya gwamnati, yana danganta kiransa da abin da ya bayyana a matsayin ƙarin wahalhalun tattalin arziki
  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC ya yi alkawarin cewa idan aka zaɓe shi, zai dawo da tallafin fetur tare da ɗaukar matakan ƙarfafa tsaro a ƙasar
  • Atiku ya kuma bukaci magoya bayan ADC su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a da kuma kare ƙuri’unsu a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Ondo - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bukaci ’yan Najeriya su zaɓi sabuwar gwamnati a 2027, yana mai danganta kiransa da ƙarin matsin tattalin arziki da ake fuskanta a ƙasar.

Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na African Democratic Congress (ADC), ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Akure, babban birnin Jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Gwamnan Benue ya tsokano fada, Kwankwaso ya yi masa raddi mai zafi

Atiku ya soki gwamnatin Tinubu
Atiku Abubakar na gabatar da jawabi Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Ya yi magana ne yayin tarbar tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Ondo na jam’iyyar PDP, Eyitayo Jegede, da magoya bayansa da suka koma ADC, cewar rahoton jaridar TheCable.

Atiku ya yi alkawarin dawo da tallafin fetur

Atiku ya ce ADC za ta samar da wata gwamnati da za ta mayar da hankali kan matsalar tsaro da wahalhalun tattalin arziki idan aka ba ta damar jagorantar ƙasar a 2027.

Ya kuma yi alkawarin dawo da tallafin fetur, tare da tabbatar da cewa babu wani yanki na Najeriya da zai kasance cikin rashin tsaro idan aka zaɓi jam’iyyar.

“Mun himmatu wajen dawo da tallafi, sannan mun himmatu wajen dawo da tsaro a faɗin ƙasar nan. Idan aka zaɓe mu, babu wani ɓangare na ƙasar da zai sake jin rashin tsaro,” in ji Atiku.

Ya soki APC kan tattalin arziƙi

Atiku ya kuma yi magana kan lokacin da ya yi Mataimakin Shugaban Ƙasa tsakanin 1999 da 2007, yana mai cewa a wancan lokacin Najeriya ta kasance cikin manyan tattalin arziƙin Afirka.

Kara karanta wannan

An yi wa su Kwankwaso alƙawarin ƙuri'u miliyan 10 a zaben shugaban kasa na 2027

Ya tambayi abin da ya haifar da koma bayan da ya ce ƙasar ta samu, inda ya ɗora alhakin hakan kan jam’iyyar APC.

“Kun san abin da muka yi tsakanin 1999 zuwa 2007. Mun mayar da Najeriya ta kasance mafi kyawun tattalin arziƙi a Afirka. Yau muna matsayi na biyar. Wa ya ɗauki alhakin mayar da mu baya? Ashe ba APC ba ce?
“Wannan shi ne lokacin da za mu kawar da su. Kuma akwai wannan sananniyar magana yanzu cewa Tinubu ya tafi.” In ji shi.

Atiku ya kawo zaɓen Osun a matsayin misali

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma ambaci zaɓen gwamnan Osun da aka gudanar a watan Agustan 2026, yana mai cewa yadda masu zaɓe suka fito da kuma ƙoƙarin kare ƙuri’u na da muhimmanci.

Ya bukaci magoya bayan ADC su yi irin wannan yunƙuri a sauran jihohi a zaɓen 2027.

Atiku ya ce jam’iyyar za ta gina ƙarfinta ne daga matakin ƙasa, sannan ya bayyana cewa komawar Jegede da magoya bayansa ADC za ta ƙara wa jam’iyyar ƙarfi a Ondo.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da Obi sun samu babbar dama a kwamitin yakin neman zaben NDC

David Mark ya nemi ƙara wayar da kan jama’a

Shugaban ADC na ƙasa, David Mark, wanda Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Rauf Aregbesola, ya wakilta, ya bukaci mambobin jam’iyyar su ƙara himma wajen neman goyon bayan jama’a tun daga matakin ƙasa.

Mark ya umurci mambobin jam’iyyar da su riƙa zuwa gida-gida domin neman ƙuri’un ’yan takarar ADC.

Atiku ya bukaci a kayar da Tinubu
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taro Hoto: @atiku
Source: Twitter

Atiku ya sa El-Rufai a kwamitin kamfen

A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar, ya naɗa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a cikin kwamitin yaƙin neman zaɓensa na jam’iyyar ADC.

Dan takarar shugaban kasar na ADC ya tabbatar da cewa El-Rufai zai kasance mataimakin shugaban kwamitin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng