Manyan Labarai A Yau
Wasu mutanen mazabar Kaduna North sun kai ƙorafi ga NDLEA kan zargin shan hodar iblis da ake yi wa Bello El-Rufai, inda suka nemi gudanar da bincike mai zaman kansa.
Omoyele Sowore ya musanta rahoton da ya alakanta shi da shawarwarin haɗa ’yan takarar shugaban ƙasa domin samar da ɗan takara guda na adawa a 2027.
Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin kawo ƙarshen biyan tallafin wutar lantarki a Najeriya daga 2027 domin samar da tsarin da zai dawwama a ɓangaren wutar lantarki.
Ƙungiyar NOSCEF ta yi kira ga Shugaba Tinubu ya janye ƙarin farashin man fetur, tana cewa matakin zai ƙara tsananta halin ƙuncin tattalin arzikin ’yan Najeriya.
Hukumar Hisbah ta Kano ta kama mai TikTok Ukasha Yahaya, wanda aka fi sani da UK International, kan bidiyon da ya nuna yana rungume da mata da yin wanka tare da su.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar kakaba wa Tarayyar Turai haraji mai tsanani ko dakatar da cinikayya idan EU ta ƙara kusantar Kanada.
Peter Obi ya ƙarfafa gwiwar ’yan Najeriya su saka jari a IPO na matatar Dangote, yana mai yabawa zuba jarin Aliko Dangote a masana’antun da dama.
Obidient Movement ta nemi INEC ta yi bayani kan inda Shugaban Hukumar Joash Amupitan yake da kuma dalilin da ya sa Rhoda Gumus ta wakilce shi a wani taro.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙalubalanci Peter Obi kan ikirarinsa na barin Anambra ba tare da bashi ba, ta nemi ya janye daga takarar 2027 idan an tabbatar da akasin haka.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari