Iran Ta Shammaci Amurka, Ta Lalata Manyan Jiragen Yakin da Ake Ji da Su
- Rundunar IRGC ta Iran ta ce ta lalata jiragen yaƙin Amurka a wani hari da ta kai sansanin al-Azraq da ke kasar Jordan
- Rundunar ta ce harin ya biyo bayan wani farmakin Amurka a tsibirin Qeshm da ya kashe iyaye biyu da ɗansu
- Hakazalika, IRGC ta kuma ce wasu daga cikin dakarunta uku sun mutu a wani harin makami mai linzami da Amurka ta kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Iran - Rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce ta lalata jiragen yaƙin F-35 guda uku na Amurka.
Rundunar IRGC ta kuma bayyana cewa ta yi wa wasu jiragen guda uku mummunar ɓarna a wani hari da ta kai sansanin sojojin sama na al-Azraq da ke kasar Jordan.

Source: Getty Images
IRGC ta lalata jiragen yakin Amurka
Tashar Aljazeera ta ce a wata sanarwa da ta fitar, IRGC ta ce harin ya biyo bayan wani farmakin da Amurka ta kai tsibirin Qeshm, wanda ya kashe iyaye biyu da ɗansu.
Kamfanin dillancin labarai na Fars ya ruwaito cewa rundunar sararin samaniyar IRGC ta harba makamai masu linzami masu nisan zango da dama kan wani wajen ajiye jiragen sama da kuma ginin kula da jiragen a sansanin al-Azraq.
Rundunar ta ce sansanin na ɗauke da jiragen yaƙin F-35 na kasar Amurka.
IRGC ta ce an kashe jami’an Amurka
A cewar IRGC, harin ya lalata jiragen F-35 guda uku gaba ɗaya tare da yi wa wasu uku mummunar ɓarna.
Rundunar ta kuma ce an kashe wasu jami’an abokan gaba da ma’aikatan fasaha da kula da jiragen sama a harin.
IRGC ta ce:
“Yankinmu ba wurin zama ba ne ga rundunar da ke kashe jarirai, wadda ke kisan gilla ga iyalai marasa laifi cikin dare yayin da suke barci.”
Rundunar ta ƙara da cewa za ta ci gaba da fafutukar da take yi tare da Jordan har sai an kori “mamaye na ƙarshe daga Amurka” daga ƙasashen Musulmi.
IRGC ta rasa dakarunta uku
Hakazalika, rundunar IRGC ta ce dakarunta uku sun mutu sakamakon wani harin makami mai linzami da Amurka ta kai.
Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito cewa reshen IRGC na lardin Zanjan mai suna Ansar al-Mahdi ya bayyana sunayen waɗanda suka mutu.
An bayyana sunayensu da Mahmoud Mollajabari da Mohammadreza Cheraghi da Jamal Amiri.

Source: Twitter
Rundunar ta ce sun mutu ne ranar 30 ga Yuli yayin da suke “kare iyakokin Iran da jama’arta” a wani hari da ta bayyana a matsayin “mummunan farmaki daga gwamnatin Amurka da ta kira ta masu aikata ta’addanci.”
IRGC ta miƙa ta’aziyyarta ga jagoran addini na Iran da iyalan waɗanda suka mutu da kuma al’ummar ƙasar. Haka kuma, rundunar ta yi Allah-wadai da harin.
Amurka ta kai hare-hare a Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Amurka ta CENTCOM, ta bayyana cewa ta kai hare-haren sama kan Iran.
A cewar rundunar CENTCOM, hare-haren martani ne ga yunkurin harba makamai masu linzami da aka yi jiya kan dakarun Amurka da ke Jordan.
Asali: Legit.ng

