An Yi Walƙiya: ADC Ta Nemi Tinubu Ya Yi wa El Rufa'i Yadda aka Yi wa Gwamnatin Osun
- ADC ta ce umarnin da Tinubu ya bai wa EFCC ya nuna hukumar ba ta da cikakken 'yancin gudanar da aikinta
- Jam'iyyar ta kalubalanci ikirarin cewa akwai umarnin kotu da EFCC ta dogara da shi wajen dakatar da asusun gwamnatin Osun
- ADC ta bukaci Tinubu ya yi irin wannan katsalandan a shari'ar Nasir El-Rufai idan da gaske yana son adalci ta tabbata a mulkinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jam'iyyar ADC ta zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da fallasa cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ba ta gudanar da aikinta cikin cikakken 'yanci ba, bayan ya umurci hukumar ta janye matakin daskarar da asusun gwamnatin jihar Osun.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam'iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi ya fitar, ADC ta ce tana maraba da janye matakin.
Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa sai dai bayanin da shugaban ƙasa ya bayar ya haifar da sabbin tambayoyi fiye da amsoshi game da aikin EFCC.
ADC ta kalubanci Tinubu
Daily Post ta ruwaito cewa jam'iyyar ta ce idan shugaban ƙasa na da ikon umartar EFCC ta janye daga shari'a saboda tasirin siyasa kan zaɓe, hakan na nuna yana da ikon ba hukumar umarni kan sauran ayyukanta ma.
ADC ta ce hakan ya rushe hujjar da ake ta yi cewa EFCC da sauran hukumomin yaƙi da cin hanci suna gudanar da ayyukansu ba tare da katsalandan daga fadar shugaban ƙasa ba.

Source: Twitter
Har ila yau, jam'iyyar ta ƙaryata ikirarin Tinubu cewa EFCC ta daskarar da asusun gwamnatin Osun ne bisa umarnin kotu kamar yadda hukumar ta sanar.
ADC ta nemi a saki El-Rufa'i
Jam'iyyar ta ce a duk bayanan da hukumar ta fitar tun farko, EFCC ta jingina matakin ne da ikon da doka ta ba ta da kuma aikinta na hana aukuwar laifi, ba tare da ambaton wata umarnin kotu ba.
Saboda haka, ADC ta bukaci shugaban ƙasa ya bayyana inda wannan umarnin kotu ya fito da kuma dalilin da ya sa EFCC ba ta taɓa ambatonsa ba a cikin bayananta ko hirarrakin da ta yi da kafafen yaɗa labarai.
Jam'iyyar ta ce ko dai an ba shugaban ƙasa bayanin da ba daidai ba ne, ko kuma shi da kansa ya bayyana bayanan da ba su dace ba, inda ta ce dukkan zabin biyu abin damuwa ne.

Source: Twitter
ADC ta kuma ce umarnin da Tinubu ya bai wa EFCC ta dakatar da shari'ar ya saɓa da ikirarin da gwamnati ke yi cewa hukumomin yaƙi da cin hanci suna aiki ba tare da tsoma bakin siyasa ba.
Jam'iyyar ta ce abin mamaki ne yadda shugaban ƙasa ya fitar da sanarwar da kansa maimakon ta fito ta hanyoyin sadarwa na fadar shugaban ƙasa, tana mai cewa hakan ya ƙara jefa shakku a zukatan jama'a.
Jam'iyyar ta ƙara da cewa idan shugaban ƙasa ya nuna yana da iko, ya kamata ya yi irin wannan umarni ga ICPC da lauyoyinta su daina adawa da neman belin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai.
ADC ta yi rashi
A baya, kun samu labarin cewa Sanata Mohammed Onawo ya sauya sheka daga jam'iyyar ADC zuwa APM yayin da ake shirye-shiryen babban zabe mai zuwa
Dan Majalisar dattawan ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar gwamnan Jihar Nasarawa karkashin inuwar jam'iyyar a babban zaɓe. 2027.
Ya ce rikice-rikice da zargin magudi a zaɓen fidda gwani na ADC ne suka sa ya fice dga jam'iyyar hadaka domin a sama wa kai da magoya baya mafita.
Asali: Legit.ng


