An Zo Wajen: Shugaba Trump Ya Yi Magana kan Batun Karancin Makaman Amurka

An Zo Wajen: Shugaba Trump Ya Yi Magana kan Batun Karancin Makaman Amurka

  • Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi magana kan rahotannin da ke cewa Amurka na fuskantar karancin wasu muhimman makamai
  • Donald Trump ya bayyana cewa kamfanonin tsaro na ƙara gina masana'antu domin bunƙasa samar da makamai a Amurka
  • Shugaban kasar na Amurka ya kuma yi barazanar hukunta waɗanda ya zarga da tona bayanan sirri, yana mai cewa ana farautarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Washington, DC, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi martani kan rahotannin da ke cewa kasarsa na fuskantar matsalar karancin makamai.

Shugaba Trump ya yi watsi da rahotannin kafafen yaɗa labarai da ke cewa ajiyar makamai masu linzami ta ma'aikatar tsaron Amurka (Pentagon) na raguwa.

Trump ya ce Amurka na da makamai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaban kasar na Amurka ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Alhamis, 5 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Asirin Amurka ya tonu, an fadi yadda makamanta ke karewa a yaki da Iran

Trump ya ce sojojin Amurka har yanzu suna da dimbin makamai, kuma ana ci gaba da ƙara yawan samar da su.

Trump ya ce Amurka na da isassun makamai

A cikin saƙon da ya wallafa, Shugaba Trump ya ce Amurka na da tarin makamai, musamman wasu nau'o'i da ake buƙata.

"Amurka na da dimbin makamai, musamman wasu nau'o'insu." In ji Shugaba Trump.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da ƙera sababbin makamai tare da jigilar su zuwa Amurka idan buƙatar hakan ta taso.

"Ana ƙera makamai da yawa tare da tura su zuwa Amurka idan an buƙata. Kamfanonin tsaro na gina masana'antu da cibiyoyin samar da kayayyaki mafi yawa a tarihin ƙasarmu."

- Shugaba Donald Trump

Trump ya yi barazana ga masu tona bayanan sirri

Trump ya kuma soki mutanen da ake zargin sun bai wa kafafen yaɗa labarai bayanan da suka haifar da rahotannin.

Ya bayyana waɗannan bayanai a matsayin masu illa ga ƙasa, tare da gargadin cewa waɗanda suka fitar da su za su fuskanci hukunci.

Kara karanta wannan

Rahoto daga Isra'ila ya tona asirin yadda Trump ya shiga tsaka mai wuya kan Iran

"Ana farautar masu tona waɗannan bayanai da za a iya ɗauka a matsayin cin amanar ƙasa."

- Shugaba Donald Trump

Shugaban kasar na Amurka ya ƙara da cewa:

"Za a nemi a yanke musu hukuncin ɗaurin dogon lokaci a gidan yari."

Kalaman Trump na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun bayyana cewa sojojin Amurka sun yi amfani da mafi yawan makaman kariya daga hare-haren makamai masu linzami tun bayan fara rikicin da Iran.

Trump ya yi magana kan rashin makaman Amurka
Shugaba Donald Trump na jawabi a wajen taron G7 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya yi maganar yarjejeniya da Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan yiwuwar kulla yarjejeniya da Iran dangane da bude mashigar ruwa ta Hormuz.

Shugaban kasar na Amurka ya kuma yi gargadin cewa za a kai wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran hari mai tsanani idan tattaunawar ta gaza samar da sakamakon da ake bukata.

Mai girma Donald Trump ya yi barazanar kai wa Iran hari “mai tsanani,” inda ya nuna cewa za a iya kai hare-hare kan muhimman abubuwan more rayuwar jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng