Minista Ya Cire Tsoro, Ya Fadi Babban abin da ke Rura Wutar Ta'addanci a Najeriya

Minista Ya Cire Tsoro, Ya Fadi Babban abin da ke Rura Wutar Ta'addanci a Najeriya

  • Ministan Yaɗa Labarai ya ce labaran karya, bayanan bogi da kalaman ƙiyayya na ƙarfafa masu laifi tare da haddasa rashin tsaro a Najeriya
  • Gwamnati ta ce magance matsalar tsaro na buƙatar haɗin kan gwamnati, al'umma, sarakuna, kafafen yaɗa labarai da masu ruwa da tsaki
  • An kafa cibiyar wayar da kai kan kafofin sadarwa da bayanai tare da UNESCO domin koyar da matasa yadda za su gano labaran karya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Abia - Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Mohammed Idris, ya yi gargaɗin cewa yada labaran karya, bayanan bogi da kalaman ƙiyayya sun zama makaman da masu laifi ke amfani da su wajen ƙara ta'addanci da haddasa rashin tsaro a Najeriya.

Idris ya bayyana hakan ne a taron tsaro na shiyyar Kudu maso Gabas da aka gudanar a Umuahia, jihar Abia, wanda Ma'aikatar Tsaro ta shirya tare da Ƙungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta lallaba Saudiyya, tana so a taimaka wa Najeriya kan karatun allo

Ministan yada labarai ya ce labaran karya ne ke kara rura ta'addanci a najeriya
Ministan yada labarai, Mohammed Idris yana jawabi ga 'yan Najeriya. Hoto: @HMMohammedIdris
Source: Twitter

Tsaro ba aikin gwamnati kaɗai ba ne

Ministan ya ce tsaro ba zai samu nasara ba idan gwamnati da jami'an tsaro kaɗai suka ɗauki nauyinsa, yana mai jaddada cewa dole ne al'umma, sarakunan gargajiya, shugabannin addini, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa kai, in ji rahoton Vanguard.

Ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na aiwatar da dabarun tsaro da suka haɗa da aikin soja, tattara bayanan sirri, gyaran tsarin shari'a da kuma bunƙasa tattalin arziki.

A cewarsa, gwamnati ta kuma ci gaba da zuba jari a hanyoyi, wutar lantarki da fasahar zamani domin ƙarfafa ci gaba da rage yawan aikata laifuka.

Labaran karya na ƙara rashin tsaro

Mohammed Idris ya ce yaƙin rashin tsaro ba ya gudana a filin daga kawai, har ma yana gudana a fagen yaɗa bayanai.

“Masu aikata laifuka na amfani da labaran karya, bayanan bogi da kalaman ƙiyayya wajen tayar da tsoro, raba kan al'umma da raunana haɗin kan ƙasa,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa na neman hada Obi fada da ƙabilarsa, ta fadi yadda zai cutar da su

Punch ta rahoto ya ce bayanan ƙarya da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na iya jefa jama'a cikin firgici tare da taimaka wa ƙungiyoyin masu laifi cimma manufofinsu.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris na jawabi a taron tsaro na shiyyar Kudu maso Gabas da aka gudanar a Umuahia, jihar Abia.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris na jawabi a taron tsaro na shiyyar Kudu maso Gabas da aka gudanar a Umuahia, jihar Abia. Hoto: @HMMohammedIdris
Source: Twitter

Dalilin kafa MILI tare da UNESCO

Saboda haka, ya bayyana cewa Ma'aikatar Yaɗa Labarai tare da haɗin gwiwar UNESCO sun kafa cibiyar wayar da kai kan kafofin sadarwa da bayanai (MILI) domin koya wa matasa yadda za su tantance sahihin bayani da kuma kauce wa yaudarar intanet.

Ministan ya kuma yi kira ga 'yan jarida su riƙa gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa da kishin ƙasa, yana gargadin cewa rahotannin da suka wuce kima ko marasa tabbaci na iya amfanar masu aikata laifuka maimakon taimaka wa ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya.

"Fulani ba 'yan ta'adda ba ne"

A wani labari, mun ruwaito cewa, sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya ce bai dace a rika kiran masu garkuwa da "Fulani makiyaya" ba.

Mai alfarmar ya ce Fulani a shirye suke su hada kai da gwamnati wajen korar masu aikata miyagun ayyuka daga matsugunansu.

A hannu daya, kungiyar Fulani ta MACBAN ta sake yin Allah wadai da ta'addanci, garkuwa da mutane da satar shanu a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com