Shugaba Tinubu Ya Rusa Kwamitin da Obasanjo Ya Kafa kan Kadarorin Gwamnatin Tarayya
- Shugaba Bola Tinubu ya amince da rusa Kwamitin Aiwatar da Ayyukan Fadar Shugaban Kasa (PIC) kan sayar da kadarorin gwamnatin tarayya
- Ministan shari’a, Lateef Fagbemi, zai jagoranci dukkan harkokin da suka shafi ayyukan kwamitin da aka rushe
- Gwamnatin tarayya ta ce kwamitin ya wuce iyakar aikinsa, lamarin da ya jawo kararraki a sassan kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da rusa Kwamitin Aiwatar da Ayyukan Fadar Shugaban Kasa (PIC) nan take.
Kwamitin na PIC da Shugaba Tinubu ya rushe yana kula da sayar da kadarorin gwamnatin tarayya.

Source: Facebook
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a shafinsa na X a ranar Alhamis, 30 ga watan Yulin 2026.
Sanarwar ta ce daga yanzu, Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi, zai jagoranci dukkan harkokin da suka shafi ayyukan kwamitin da aka rushe.
An ce umarnin da aka bai wa ministan shari’a na jagorantar ayyukan PIC ya fara aiki tun daga ranar 5 ga Nuwamba, 2025.
Dalilin rusa kwamitin
Bayo Onanuga ya ce gwamnatin tarayya ta yanke hukuncin cewa babu sauran bukatar ci gaba da aikin kwamitin.
Sanarwar ta ce:
“Bayan nazari mai zurfi, gwamnati ta lura cewa ayyukan PIC sun wuce iyakar aikin da aka kafa shi domin yi, lamarin da ya haifar da kararraki da dama a fadin kasar nan. Saboda haka, babu sauran dalilin da zai tabbatar da ci gaba da kasancewar kwamitin.”
Yadda aka kafa PIC
An kafa kwamitin PIC ne a shekarar 2000, a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
An dora wa kwamitin alhakin sa ido kan sayarwa, ba da haya da mayar da kadarorin filaye na gwamnatin tarayya zuwa hannun wasu, karkashin tsarin gwamnati na sauya yadda ake biyan alawus da samar da wasu fa’idoji ga ma’aikata.
Ministan gidaje na lokacin ne ke jagorantar kwamitin, tare da wakilai daga ma’aikatun sufuri, shari’a, lafiya da noma, da kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya.
Farfesa P. T. Ahire, wanda a lokacin yake mataimakin darakta a ofishin sakataren gwamnatin tarayya, shi ne sakataren farko na kwamitin.
Sauran mambobin kwamitin sun fito ne daga bangaren gwamnati da kuma masu zaman kansu.

Source: Twitter
Tarihin binciken kwamitin
Sanarwar ta tuna cewa a ranar 22 ga Maris, 2001, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da kafa wani kwamitin bincike.
An ce an kafa kwamitin ne domin samar da takardar gwamnati mai dauke da matakan da za su jagoranci aiwatar da shawarwarin da ya bayar.
Kwamitin binciken ya shafe watanni 21 yana aiki kafin ya gabatar da rahotonsa.
Sanarwar ta kuma umarci tsohon sakataren PIC, B. S. Dutsin-Ma, da ya daina wakiltar kwamitin ko gwamnatin tarayya a duk wani al’amari da ya shafi ayyukansa.
Kwankwaso ya yabawa Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Alhaji Iliyasu Musa Kwankwaso, ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan amincewa da gyaran filin jirgin sama na Kano.
Kwankwaso ya ce amincewar ta nuna kudirin Shugaba Tinubu na bunƙasa Arewa da tattalin arzikinta, yana mai cewa aikin zai ƙara haɓaka harkokin kasuwanci a faɗin yankin.
Asali: Legit.ng

