An Sanya Lokacin Bikin Auren Gata, Gwamna Abba Ya Yi Nasiha ga Ma'aurata 1,500

An Sanya Lokacin Bikin Auren Gata, Gwamna Abba Ya Yi Nasiha ga Ma'aurata 1,500

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da shawara ga ma’aurata 1,500 da za su shiga shirin auren gata na 2026
  • Gwamnatin Kano za ta tallafa wa ango da amarya da kudade da kayan gida domin fara rayuwar aure
  • Za a daura auren ranar Juma’a a Babban Masallacin Juma’a na Kano da kuma hedikwatar kananan hukumomi 44 na jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi muhimmin kira ga mutanen da za su gajiyar auren gata na shekarar 2026.

Gwamna Abba ya bukaci ma’aurata 1,500 da za su shiga shirin auren gata na jihar na shekarar 2026 da su gina aurensu bisa amana, hakuri, mutunta juna da kuma tsoron Allah.

Za a yi auren gata a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 6 ga watan Agustan 2026, yayin wani shirin horaswa da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta shirya wa ma’auratan da za su yi aure a dakin taro na Coronation Hall, a matsayin wani bangare na shirye-shiryen gudanar da auren.

Kara karanta wannan

Adeleke ya zargi EFCC da shirin yi wa gwamnatinsa illa gabanin zaɓen Osun

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar, cewar rahoton The Punch.

Abba Yusuf ya yi bayani kan muhimmancin aure

Gwamnan, wanda Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Aminu Daurawa, ya wakilta, ya bayyana aure a matsayin ibada mai tsarki da ke bukatar jajircewa, tausayi da fahimtar juna daga bangarorin ma’aurata.

Ya shawarci masu shirin yin auren da su kasance masu biyayya ga juna, su yi hakuri a lokacin kalubale, sannan su rika warware sabani ta hanyar tattaunawa maimakon rikici.

An rawaito gwamnan yana cewa:

"Duk wani aure mai nasara yana ginuwa ne kan cika hakki da nauyin da ya rataya a wuyan kowane ma’auraci, domin zaman lafiyar iyali shi ne ginshikin ci gaban kowace al’umma."

Ya kara da cewa iyalai masu karfi suna taimakawa wajen samar da zaman lafiya a cikin al’umma, tare da kira ga ma’auratan su rungumi dabi’un da za su inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidajensu.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya ƙaddamar da aikin da ba a taɓa ganin irinsa ba a Arewacin Najeriya

Malamai sun yi wa ma’aurata nasiha

Shirin horaswar ya kunshi lakcoci daga malamai da kwararru kan batutuwan aure, hakkin ma’aurata, nauyin iyali da hanyoyin warware rikice-rikicen aure.

Sheikh Ali Aliyu Abubakar ya gabatar da lakca mai taken "Hikimar Aure a Musulunci," yayin da Farfesa Ibrahim Mu’azzam Mai Bushira ya yi bayani kan "Hakkoki da Nauyin Ma’aurata a Musulunci."

Haka kuma, Sheikh Muhammad Nur Arzai ya yi wa mahalarta bayani kan musabbabin sabanin aure da hanyoyin warware shi bisa koyarwar Musulunci.

Sauran masu gabatar da jawabi sun hada da Barrister Habibu Dan Almajiri, Sheikh Ibrahim Shehi Shehi Mai Hula, Dr. Zahara’u Muhammad Umar da Dr. Khadija Sagir Suleiman, inda suka yi bayani kan bangarorin shari’a, zamantakewa, addini da lafiya da suka shafi aure.

Za a yi airen gata a Kano
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamnati ta tanadi tallafi ga angwaye da amare

A matsayin tallafin gwamnati, kowane ango zai karbi yadi 10 na shadda, hula, buhun shinkafa da jarkar man girki domin taimaka masa wajen fara rayuwar aure.

Kara karanta wannan

Fitaccen dan TikTok ya ga ta kansa a Kano bayan ya saki bidiyo kan 'kwanciya da mata'

Ita kuma kowace amarya za ta karbi N200,000 domin sadaki da tallafin fara sana’a, tare da kayan daki da suka hada da gado, katifa, wardrobe, madubi, bargo, zanin gado da tabarmar falo.

Yaushe za a daura auren?

Za a daura auren ranar Juma’a a Babban Masallacin Juma’a da ke birnin Kano, tare da gudanar da irin wannan biki a lokaci guda a hedikwatar kananan hukumomi 44 na jihar.

Shirin zai kare ne ranar Lahadi da rabon kayan daki da sauran kayayyakin tallafi ga sabbin ma’aurata.

An daura auren gata a Kebbi

A wani labarin kuma, kun ji cewa an yo bikin ɗaura auren ma'aurata 300 da aka yi wa auren gata a filin wasa na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi.

Gwamnan jihar Kebbi, Dr Nasir Idris, ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da gudanar da shirin auren gata na shekara-shekara domin tallafa wa marasa galihu a faɗin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com