Shin da Gaske Ma'aikatar Kudi Ta Bukaci Sababbin Ma'aikata Su Biya N50,000?
- Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta yi martani kan saƙon da ke neman sababbin ma’aikata su biya N50,000
- A cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta bayyana cewa ba a biyan kuɗin gudanarwa ko na fara aiki a tsarin ɗaukar ma’aikata
- Hakazalika, ma'aikatar kudin ta shawarci jama’a su guji biyan kuɗi ko bayyana bayanansu ga masu wannan salo na damfara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ta nesanta kanta da wani saƙon damfara da ake yaɗawa sababbin ma’aikatan da aka ɗauka aiki, wanda ke umartarsu su biya N50,000 a matsayin kuɗin gudanarwa kafin su fara aiki.
Shugabar Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ma’aikatar, Efe Ovuakporie, ta bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 29 ha watan Yulin 2026.

Source: Facebook
Jaridar Tribune ta ce Efe Ovuakporie tace masu damfara ne suka ƙirƙiri saƙon domin yaudarar masu neman aiki ta hanyar amfani da sunan Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya.
Abin da saƙon bogin ya ƙunsa
A cewar sanarwar, saƙon ya yi iƙirarin ƙarya cewa Sashen Gudanar da Harkokin Ma’aikata ya umarci sababbin ma’aikata su biya kuɗin gudanarwa kafin su fara aiki.
Sai dai ma’aikatar ta bayyana cewa ba ta bayar da irin wannan umarni ba, yayin da ta kuma jaddada cewa saƙon bai fito daga wani ofishi ko jami’in Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ba.
Tsarin ɗaukar ma’aikatan gwamnati
Ma’aikatar ta ce ana ɗaukar ma’aikata a Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya ne bisa tsare-tsare da ƙa’idojin Hukumar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.
“Babu wani mataki a tsarin ɗaukar ma’aikata, tattara takardu ko shigar da sababbin ma’aikata aiki da ake buƙatar masu neman aiki ko waɗanda aka ɗauka su biya kuɗin gudanarwa, sarrafa takardu ko na fara aiki.” In ji ta
Saboda haka, ma’aikatar ta shawarci masu neman aiki da sauran jama’a su yi watsi da saƙon damfarar, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Haka kuma, ta gargaɗe su da kada su biya wani kuɗi ko su bayyana bayanansu na sirri da na kuɗi ga mutanen da ke bayan wannan damfara.
An nemi a kai rahoton masu damfara
Ma’aikatar ta buƙaci duk wanda ya samu irin wannan saƙo ko yake da bayanan da za su taimaka wajen gano waɗanda ke da hannu a damfarar ya kai rahoto ga hukumomin tsaro da suka dace.
Ta ce ana iya sanar da ma’aikatar ta hanyoyin sadarwarta na hukuma domin taimakawa wajen gano masu aikata laifin.

Source: Twitter
Sanarwar ta ce Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya za ta ci gaba da tabbatar da gaskiya, adalci da riƙon amana a dukkan matakan ɗaukar ma’aikata.
Ta ƙara da cewa za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin da suka dace domin kare jama’a daga ayyukan damfara da ake yi da sunanta.
Tinubu ya amince da aikin N46bn a MAKIA
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 46 domin gyara tashar jirgin sama ta Malam Aminu Kano (MAKIA).
Shugaba Tinubu ya amince da kudaden ne domin sake shimfiɗa da kuma sake gina titin saukar jiragen sama na biyu a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano.
Asali: Legit.ng

