Bincike Ya Dauki Zafi, Sunayen Ministocin Tinubu 10 Sun Fito a Batun Hukumar Bogi, PFIPC
- FRSC ta ta bayyana aka saka Shugaba Tinubu da ministoci a matsayin mambobin majalisar gudanar ta hukumar PFIPC a shafinta na intanet
- Kwamitin Majalisa ya ce hakan ya kamata ya tayar da shakku kan sahihancin hukumar wacce bincike ya nuna ta bogi ce
- FRSC ta ce ta yi rajistar motoci bakwai bayan ta karɓi takardu da kuma kuɗin gwamnati ta hanyar REMITA
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), Shehu Mohammed, ya gurfana a gaban Kwamitin Bincike na Majalisar Wakilai kan batun hukumar bogi.
Ya shaida wa kwamitin cewa Prince Adeyemi Adeniyi Matthew ya saka sunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da wasu manyan jami'an gwamnati a matsayin mambobin kwamitin gudanarwa na hukumar bogi watay PFIPC a shafinta na intanet.

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta ce ya bayyana hakan ne yayin zaman binciken da kwamitin ke yi kan yadda aka saka hukumar da ake zargi da kasancewa ta bogi cikin kasafin kudin shekarar 2026.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban ƙasa na da hannu a kafa hukumar bogi ta PFIPC? ICPC ta gano gaskiya
Kwamitin Majalisa ya nuna damuwa
Shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi, ya soki FRSC saboda rashin tantance sahihancin takardun da aka gabatar kafin a ba hukumar lambobin motocin gwamnati.
Ya ce takardun sun nuna Shugaba Tinubu a matsayin shugaban majalisar gudanarwa na hukumar tare da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Shugaban Babban Bankin Najeriya (CBN), Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya a matsayin mambobi.
Sunayen ministoci 10 da suka fito
Sunayen ministocin da aka gani a matsayin mambobin Majalisar gudanarwa na hukumar bogi sun hada da:
1. Ministan Abuja
2. Ministan Kuɗi
3. Ministan Sufurin Jiragen Sama
3. Ministan Noma da Tsaron Abinci
4. Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari'a
5. Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki
6. Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku
7. Ministan Harkokin 'Yan Sanda
8. Ministan Sufuri
9. Ministan Ayyuka
10. Ministan Wutar Lantarki
Gagdi ya tambayi shugaban FRSC ko irin wannan tsari yana da ma'ana, inda shugaban hukumar ya amsa da cewa, "A'a."

Kara karanta wannan
Babbar magana: An gano sababbin hukumomi 2 da aka kafa ba tare da izinin Shugaba Tinubu ba

Source: Facebook
Yadda aka yi wa motocin rajista
Shugaban FRSC ya bayyana cewa hukumar ta karɓi buƙatar rajistar motocin gwamnati daga Prince Adeyemi, wanda ya gabatar da kansa a matsayin Darakta Janar na PFIPC.
A cewarsa, FRSC ta kuma duba shafin intanet da aka nuna musu, wanda ke amfani da adireshin gwamnatin tarayya kuma ya ƙunshi bayanan da suka yi kama da na hukuma.
Mohammed ya ce bayan an biya kuɗaɗen da doka ta tanada ta hanyar tsarin REMITA, hukumar ta samar da lambobin rajista da faranti na hukuma ga motoci bakwai da aka nema, kamar yadda Leadership ta kawo.
ICPC ta wanke fadar shugaban kasa
A wani labarin, kun ji cewa hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta wanke Fadar Shugaban Kasa daga zargin hannu wajen nada Adeniyi Adeyemi ko kirkirar PFIPC.
Hukumar ta ce takardar nadin da Adeniyi Adeyemi Matthew ya gabatar ta jabu ce kuma ba ta fito daga Fadar Shugaban Kasa ba.
A nata bangaren, Fadar Shugaban Kasa ta ce ba ita ce ta kirkiri PFIPC ba kuma ba ta taba rubuta wata takarda da ta shafi kasafin kudinta ba.
Asali: Legit.ng