Jiha 1 a Arewa Ta Shirya Hada Mutane Miliyan 1 Su Zabi Tinubu a 2027

Jiha 1 a Arewa Ta Shirya Hada Mutane Miliyan 1 Su Zabi Tinubu a 2027

  • Mataimakin Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ode, ya ce jihar na da shirin samar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuri'u miliyan 1 a zaben shugaban ƙasa na 2027
  • Ya ce gwamnatin Gwamna Hyacinth Alia za ta tattara mambobin Majalisar Zartarwa ta jihar da al'ummar Benue domin tabbatar da cika wannan alƙawari
  • Ode ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake jagorantar tawagar Sashen Sadarwa na Fadar Shugaban Ƙasa, ƙarƙashin jagorancin Bayo Onanuga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Mataimakin Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ode ya bayyana cewa a shirye jiharsa ta ke ta marawa shugaba Bola Tinubu baya a zaben 2027.

Da yake amsa tambaya kan abin da Benue za ta bayar a matsayin sakamakon ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa a jihar, Ode ya ce tuni Gwamna Alia ya yi alƙawarin cewa jihar za ta bai wa shugaban ƙasa kuri'u miliyan 1.

Kara karanta wannan

"Na ji kunya": Tinubu ya ba EFCC umarnin bude asusun gwamnatin Osun da aka rufe

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na jawabi a taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Za a ba Tinubu kuri'u a Benue

Punch ta wallafa cewa mataimakin gwamnan jihar ya ce za su ba Bola Tinubu tarin kuri'u a zaben shugaban kasa da ke tafe, ya ce:

“Mun riga mun samu sanarwar da Gwamnan Jihar Benue, Mai Girma Alia, ya yi. Ya bayyana cewa Benue za ta bai wa Mai Girma Shugaban Ƙasa kuri'u miliyan 1.
“Ina ganin alhakin da ke kaina a matsayina na Mataimakin Gwamna shi ne tabbatar da cewa na tattara Majalisar Zartarwa da al'ummar Jihar Benue gaba ɗaya domin cika wannan alƙawarin da Gwamna ya yi.”

Ayyukan da aka yi a Benue

Tun da farko, yayin da yake magana a sabon mahadar hanya da aka gina a Makurdi, Ode ya danganta bunƙasar ayyukan more rayuwa a jihar da ƙarin kuɗin da jihohi ke samu daga asusun tarayya tun bayan zuwan gwamnatin Tinubu.

Ya ce kuɗin da aka ƙara rabawa jihohi na taimakawa wajen gudanar da ayyukan da za su amfani al'ummar Benue.

Kara karanta wannan

Atiku da Peter Obi sun tafka kuskure, an cire su daga barazanar da Tinubu zai fuskanta a 2027

Ya bayyana cewa:

“Wannan rabon kuɗin da ya ƙaru shi ne abin da muke amfani da shi domin amfanin al'ummar Jihar Benue. Dukiyarsu ce ta bai ɗaya, saboda haka muna son su ga ci gaba a zahiri.
“Abin da kuke gani a nan shi ne yadda ake amfani da kuɗin da ke shigowa daga asusun tarayya cikin tsari, waɗanda suka ƙaru tun bayan zuwan gwamnatin Tinubu.”
Shugaba Bola Tinubu
Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tinubu zai samu kuri'u a Gombe

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da kwamitin sulhu na jam'iyyar mai mambobi 25 domin warware rikice-rikicen cikin gida.

Gwamnan ya ce burin APC a jihar shi ne ta riƙe dukkanin kujerun da take da su tare da samar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuri'u da ba su gaza miliyan 1 ba.

Ya kuma ce jam'iyyar na son tabbatar da nasarar ɗan takararta na gwamna, 'yan takararta shida na Majalisar Dokoki ta Ƙasa da kuma 'yan takararta 24 na Majalisar Dokokin Jihar Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng