Mummunan Rikicin Kabilanci da Fulani Ya Barke a Plateau, sojoji sun taka rawa
- Rundunar sojoji ta hana wata mummunar arangama tsakanin wasu mayakan Fulani da Mwaghavul a yankin Mangu na Plateau.
- Sojojin sun kai ɗauki bayan samun rahoton musayar wuta tsakanin ƙungiyoyin biyu a kusa da kogin da ya raba Gaude da Aloghom.
- Bayan shiga tsakani, sojoji sun mamaye yankin tare da fara matakan dawo da zaman lafiya, yayin da ake kokarin hana ramuwar gayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Sojojin Sector 8, Sub-Sector 81, karkashin Operation Enduring Peace, sun hana wata arangama na fadan kabilanci.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa fadan ya barke ne tsakanin wasu da ake zargin mayakan Fulani da Mwaghavul ne a Mangu.

Source: Original
An yi harbe-harbe a ƙauyukan Plateau
Majiyoyi sun shaida wa Zagazola Makama cewa sojojin sun mayar da martani da misalin karfe 5:25 na yammacin ranar 6 ga Agusta, bayan samun rahoton harbe-harbe a bakin kogin da ya raba kauyukan Gaude da Aloghom.
Da isarsu wurin, sojojin sun gano cewa wasu dauke da makamai daga kungiyoyin biyu sun shiga musayar harbe-harbe.
Majiyoyin sun ce mayakan da ake zargin Fulani da Mwaghavul ne sun janye daga yankin tare da watsewa zuwa wurare daban-daban bayan ganin sojojin na karatowa, lamarin da ya hana arangamar kara kamari.
Bayan shiga tsakani, jami’an tsaro sun tabbatar da iko a yankin tare da fara matakan gina amincewa domin dawo da zaman lafiya.
Majiyoyin tsaro sun ce ana ci gaba da kokari tare da hadin gwiwar shugabannin al’ummomin bangarorin biyu domin rage tashin hankali da hana duk wani harin ramuwar gayya.
Majiyoyin sun kara da cewa Operation Enduring Peace na ci gaba da tabbatar da kasancewar jami’an tsaro a yankin, a matsayin wani bangare na matakan kare zaman lafiya da hana sake barkewar tashin hankali a al’ummomin da lamarin ya shafa.

Yan bindiga sun kashe ƴan gida ɗaya
Mun ba ku labarin cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe 'yan sintiri uku 'yan uwa a Tarai da ke Riyom, yayin da suke tsaron al'umma cikin dare.
Mamatan su ne Dachung Danjuma, Victor Danjuma da Nyam Danjuma, kuma an ce an kashe su nan take bayan maharan sun yi musu kwanton bauna.
Shugabannin al'umma sun bukaci jami'an tsaro su kara matakan kariya a Riyom tare da kamo wadanda suka aikata harin domin tabbatar da adalci.
Asali: Legit.ng