Badakalar PFIPC: 'Yan Sanda Sun Kasa Kawo Adeniyi gaban Majalisa, an Ji Dalili
- Rundunar ƴan sanda ta ce Prince Adeyemi Adeniyi na tsare bisa umarnin kotu yayin da ake bincike kan kafa hukumar PFIPC
- Kwamitin Majalisar Wakilai ya ce ba zai tsoma baki a binciken ƴan sanda ko shari'ar da ke gudana ba
- Ana binciken yadda PFIPC ta samu ofishi da kasafin N1.32bn duk da zargin cewa ba a kafa ta bisa doka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sufeto Janar na Ƴan Sanda (IGP), Olatunji Rilwan Disu, ya bayyana dalilin da ya sa rundunar ƴan sanda ba ta gabatar da wanda ake zargin ya ayyana shugaban hukumar PFIPC, Prince Adeyemi Adeniyi, gaban kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai.
An bayyana hakan ne a cikin wata wasiƙa da aka aikawa kwamitin, wadda shugabansa, Yusuf Gagdi (APC, Plateau), ya karanta ranar Laraba, 29 ga watan Yulin 2026.

Source: Twitter
Wasiƙar ta zo ne bayan Adeniyi ya kasa bayyana a gaban ƴan majalisar kamar yadda aka umarce shi tun da farko, jaridar Tribune ta kawo labarin.
Dalilin da ya sa Adeniyi bai halarta ba
Yayin karanta wasiƙar, Gagdi ya ce rundunar ƴan sanda ta sanar da kwamitin cewa Adeniyi na ci gaba da kasancewa a tsare saboda binciken wani laifi da ake yi kan zargin haɗin baki.
“Muna da ƙa'ida da muke bi. Muna sane da hakan. Kashi na farko na binciken ya shafi haɗin baki da yin takardun bogi, kuma wannan ne ya sa aka tsare mutumin. Muna mutunta ƙa'idar raba iko tsakanin hukumomi.”
- Yusuf Gagdi
Gagdi ya ce ya karanta wasiƙar ƴan sanda a bainar jama'a ne domin hana yaɗuwar rahotannin da za su nuna cewa Adeniyi ya yi watsi da sammacin kwamitin, rahoton The Punch ya nuna hakan.
“Na yanke shawarar karanta wasiƙar domin kada ƴan jarida su ce mutumin ya ƙi bayyana. Muna da matakai da ƙa'idojin da muke bi.”
- Yusuf Gagdi
Umarnin kotu ya hana gabatar da shi
A cewar Gagdi, IGP ya bayyana cewa ba za a iya gabatar da Adeniyi a gaban kwamitin ba saboda ana tsare da shi bisa ingantaccen umarnin kotu.
“IGP ya ce mutumin yana tsare ne bisa umarnin kotu. Ya bayyana cewa kotu ta bayar da umarnin tsare shi, kuma wannan ne dalilin da ya sa yake hannun hukuma.”
“Saboda haka, kafin a kawo shi Majalisar Dokoki ta Ƙasa, dole ne a soke ko a janye umarnin kotun.”
- Yusuf Gagdi
Kwamitin ya ce ba zai tsoma baki ba
Shugaban kwamitin ya ce ba za su tsoma baki a binciken da ƴan sanda ke yi ko shari'ar da ke gudana ba.
“Ba za mu iya yin katsalandan a binciken da ke gudana ba. Muna yaba ayyukan da Sufeto Janar na Ƴan Sanda, rundunar ƴan sanda, DSS, ICPC, EFCC da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ke yi, kuma ba za mu kawo cikas ga wannan tsari gaba ɗaya ba.”

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa na neman hada Obi fada da ƙabilarsa, ta fadi yadda zai cutar da su
- Yusuf Gagdi
Gagdi ya ce kwamitin zai ci gaba da aiki tare da ƴan sanda da sauran hukumomin da abin ya shafa yayin da binciken ke gudana.
“Za mu ci gaba da rubuta muku domin samun ƙarin rahotanni da fayyace wuraren da har yanzu akwai ruɗani. Zuwa mako mai zuwa, za mu iya gabatar da rahotonmu yayin da za a ci gaba da sauraron wannan batu.”
- Yusuf Gagdi

Source: Facebook
Yadda aka kafa hukumar PFIPC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Akanta-Janar na tarayya ya bayyana hanyar da aka bi wajen kafa hukumar PFIPC.
Akanta-Janar na tarayya ya bayyana cewa an yi amfani da wasiƙar fadar shugaban ƙasa ta bogi wajen samun amincewar hukuma ga “hukumar bogin”.
Asali: Legit.ng
