Gwamnatin Tinubu Ta Bayyana Dalilin da Ya Sa 'Yan Najeriya Suka Tsunduma cikin Talauci

Gwamnatin Tinubu Ta Bayyana Dalilin da Ya Sa 'Yan Najeriya Suka Tsunduma cikin Talauci

  • Ministan kudi Taiwo Oyedele ya ce gyaran tattalin arzikin gwamnatin Bola Tinubu ba zai iya kawo sauyi nan take ba saboda cire tallafin mai ya haifar da sabon tsarin tattalin arziki
  • Oyedele ya ce talauci ya karu bayan cire tallafin mai, amma hakan ya kasance sakamakon gyaran da ake bukata domin kawo karshen almubazzaranci da rashawa
  • Ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya fara nuna alamun farfadowa a shekarar 2025, tare da alkawarin gwamnati za ta bayyana yadda aka kashe kudin da aka samu daga cire tallafin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja – Ministan Kudi, Taiwo Oyedele, ya bayyana dalilin da ya sa har yanzu 'yan Najeriya ba su fara jin cikakken tasirin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar ba.

Oyedele ya ce ana ci gaba da sake fasalin tattalin arzikin kasa bayan cire tallafin man fetur, wanda ya sa har yanzu ba a fara jin cikakken amfanin gyare-gyaren ba.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya yi barazana ga Tinubu, zai yi murabus daga jam'iyya mai mulki

Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan talauci
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

A wani bidiyo da mai ba Shugaba Tinubu shawara kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafin X a ranar Alhamis, 6 ga watan Agustan 2026, Oyedele ya amsa tambayoyi a wani taro da Hukumar Wayar da Kan Jama'a ta Kasa (NOA) ta shirya.

Oyedele ya yi bayani kan karuwar talauci

Oyedele ya ce bai yarda gaba daya da rahoton Bankin Duniya cewa gyaran tattalin arziki ya kara yawan talauci ba. Sai dai ya amince cewa cire tallafin mai ba zai sa mutane su kara arziki cikin kankanin lokaci ba.

A cewarsa:

"Eh, talauci ya karu saboda ba za ka cire tallafi ba sannan mutane su kara arziki nan take. Gyaran da aka yi wani sabon tsari ne domin dakatar da yaudarar kanmu wajen tafiyar da tattalin arziki."

Ya kara da cewa Najeriya ta dade tana rayuwa cikin abin da ya kira "ruɗin kasafin kudi", don haka sai an yi gyaran da zai sa tattalin arzikin ya tsaya kan ingantaccen tushe.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta sauko bayan 'yan Katolika sun ja daga, za a tattauna

Tattalin arziki ya fara farfadowa

Ministan ya ce duk da wahalhalun farko, alkaluman shekarar 2025 sun nuna cewa tattalin arzikin kasar ya fara farfadowa.

Ya bayyana cewa ci gaban kudin shiga ga kowane mutum ya kai kusan 10% idan aka auna da dalar Amurka.

Oyedele ya ce hakan ya sanya Najeriya cikin kasashen da ke saurin rage talauci, yana mai cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kokarin tabbatar da wannan ci gaba.

Inda kudin tallafin mai suka tafi

Oyedele ya ce tambayar da ake yi kan inda kudin da aka samu bayan cire tallafin mai suka tafi tambaya ce mai muhimmanci.

Ya bayyana cewa tallafin man fetur da abin da ya kira tallafin canjin kudin waje sun kai kusan 5% na GDP.

A cewarsa, babban manufar cire tallafin ba wai tara kudi kawai ba ce, illa kawar da karkacewar tsarin tattalin arziki da kuma yaki da rashawa.

"Nan da 'yan kwanaki gwamnati za ta fitar da cikakken bayani kan yadda aka yi amfani da kudaden, saboda muna da alhakin bayyana wa 'yan Najeriya abin da muke yi. Wannan shi ne ma'anar gaskiya da rikon amana." In ji shi

Kara karanta wannan

Ma'aikata za su warwasa, Shugaba Tinubu ya shirya cika alƙawarin da ya ɗauka

Taiwo Oyedele ya yi magana kan cire tallafi
Ministan kudi, Taiwo Oyedele Hoto: @taiwooyedele
Source: Facebook

Tinubu ya kira Adeleke a waya

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban kasa a Najeriya ta tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kira Gwamna Ademola Adeleke a waya.

Shugaba Bola Tinubu ya kira gwamna Adeleke, domin tabbatar masa da umarnin da ya bayar ga hukumar EFCC bayan matakin da ta dauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng