Wata Sabuwa: Sojojin Israila Sun Yi Wa Kwamandojinsu Bore, an Ji Dalili

Wata Sabuwa: Sojojin Israila Sun Yi Wa Kwamandojinsu Bore, an Ji Dalili

  • Wasu sojoji da dama daga rundunar Givati sun bar sansaninsu da ke kudancin Isra’ila bayan rikici da kwamandansu
  • Sojojin sun bar sansanin Sde Teiman ba tare da izinin manyansu ba, inda suka bar makamansu a baya domin yin bore kan abin da aka yi masu.
  • Rahotanni sun ce lamarin ya sa bataliyar ta rasa cancantar shiga wani aikin soja da take shirin gudanarwa a Gaza

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kasar Israila - Wasu sojoji da dama daga Bataliyar Tzabar ta rundunar Givati sun bar sansaninsu da ke kudancin Isra’ila bayan rikici da kwamandansu, kamar yadda rundunar sojin Isra’ila (IDF) ta tabbatar.

Rundunar IDF ta ce sojojin sun fice daga sansanin Sde Teiman ba tare da amincewar manyansu ba, inda suka bar makamansu a baya.

Sojojin Israila sun yi bore
Shugaban sojojin Israila na duba wasu sojoji Hoto: @idfonline
Source: Twitter

Jaridar Times of Israel ta ce lamarin ya faru ne bayan kwamandan bataliyar ya yanke shawarar cire tare da lalata wasu alamomi da sojojin suka kafa a sansanin.

Kara karanta wannan

Yadda aka shirya amfani da Boko Haram, JTF domin kifar da gwamnatin Tinubu

Meyasa sojoji suka yi bore?

A cewar rundunar, alamomin da aka yi wa ado da su na dauke da abubuwan da ake zargin suna wulakanta sababbin sojojin da suka shiga rundunar.

Sai dai sojojin sun ce alamomin “wani bangare ne na al’adar bataliyar.” wadanda aka dade ana amfani da su.

Rundunar IDF ta bayyana cewa:

“Ana bincike tare da daukar matakin da ya dace kan lamarin ta hannun kwamandoji. Wannan abu bai dace da kimar rundunar IDF ba, kuma ya saba da abin da ake tsammani daga sojojinta.”

Sojoji sun kare alamomin

Ynet ta ruwaito cewa, a cewar wasu sojojin bataliyar, alamomin da aka cire sun kasance tare da su yayin yakin da suka yi a Gaza da Lebanon.

Rahoton ya ce ana gadar da alamomin daga rukuni daya na sababbin sojoji zuwa wani, kuma sojojin suna kallonsu a matsayin wani abu da ke nuna alakar da ke tsakaninsu da bataliyar da kuma al’adunta.

Kara karanta wannan

Rundunar soji ta nada sababbin kwamandoji domin yakar rashin tsaro

Bataliyar ta rasa shirin yaki

An ce sojojin rundunar kasa ta IDF sun taba yin irin wannan ficewa gaba daya daga sansaninsu a baya, sakamakon zargin rashin adalcin da ake musu a aikin soja.

Jaridar Maariv ta Isra’ila, tana mai nakalto wani jami’in soja da ba a bayyana sunansa ba, ta ce lamarin ya sa bataliyar ta rasa cancantar shiga ayyukan yaki da take shirin gudanarwa a Gaza.

Wasu sojoji sun yi bore a Israila
Sojoji na magana da Eyal Zamir Hoto: @idfonline
Source: Twitter

Haka kuma, Israel Hayom ta ruwaito cewa sojoji da kwamandojinsu sun bar sansanin Sde Teiman dauke da jakunkunansu na kashin kai, ba tare da kayan aikinsu na soja da makamansu ba, sannan suka nufi gidajensu.

An nemi a cafke Firaministan Israila

A wani labarin kuma, kun ji cew kungiyar Amnesty International ta Najeriya ta bukaci hukumomin Amurka su cafke Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.

Kungiyar ta bukaci Amurka ta mutunta hakkin dan Adam da kuma bin doka ta hanyar mika Netanyahu ga Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya (ICC).

Kiran na Amnesty na zuwa ne bayan Benjamin Netanyahu ya kai ziyara Fadar White House domin ganawa da Shugaba Donald Trump.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng