Diomande, Osimhen: Jerin 'Yan Wasan Afrika 10 mafi Tsada a Tarihin Kwallon Kafa

Diomande, Osimhen: Jerin 'Yan Wasan Afrika 10 mafi Tsada a Tarihin Kwallon Kafa

  • Real Madrid ta ɗauki ɗan wasan Ivory Coast, Yan Diomande, kan dala miliyan 144, abin da ya sa ya zama ɗan Afirka mafi tsadar ciniki a tarihi
  • Victor Osimhen ya shiga jerin sau biyu bayan cinikinsa zuwa Napoli da Galatasaray, yayin da Nicolas Pépé ya zo na biyu a jerin
  • Jerin ya nuna yadda manyan ƙungiyoyin Turai ke ci gaba da kashe kuɗaɗe masu yawa wajen sayen fitattun 'yan wasan Afirka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin wasanni, siyasa da al'amuran yau da kullum, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Madrid, Spain – Rahotanni sun bayyana cewa Real Madrid ta ɗauki matashin ɗan wasan Ivory Coast, Yan Diomande, daga RB Leipzig kan kuɗi da suka kai dala miliyan 144.

Idan aka tabbatar da wannan ciniki, Diomande mai shekara 19 zai zama ɗan wasan Afirka mafi tsadar ciniki a tarihin ƙwallon ƙafa.

Kara karanta wannan

Yadda za ku duba sunayen waɗanda hukumar Kwastam ta ɗauka aiki a 2026

Afrika na da 'yan wasa 10 mafi tsada a tarihin kwallon kafa.
Hagu zuwa dama: Nicolas Pepe na Cote d'Ivoire; Victor Osimhen na Najeriya da Yan Diomande na Ivory Coast. Hoto: Robert Cianflone, Abdulhamid Hosbas/Anadolu, NurPhoto via Getty Images
Source: Getty Images

Osimhen ya shiga jerin sau biyu

Matashin ya yi fice a kakar wasan da ta gabata tare da RB Leipzig, inda bajintarsa ta ja hankalin manyan ƙungiyoyin Turai kafin Real Madrid ta cimma yarjejeniya da shi, in ji rahoton Punch.

Tsohon ɗan wasan Arsenal, Nicolas Pépé, shi ne na biyu a jerin bayan komawarsa daga Lille zuwa Arsenal kan dala miliyan 92.

Ɗan wasan Najeriya, Victor Osimhen, ya kasance cikin jerin sau biyu, inda cinikinsa daga Lille zuwa Napoli ya kai dala miliyan 91.

Haka kuma, rahotanni sun ce komawarsa ta dindindin daga Napoli zuwa Galatasaray ta kai dala miliyan 87, lamarin da ya sa ya kasance cikin manyan 'yan wasan Afirka mafi tsadar ciniki.

Kungiyoyi sun kashe kuɗi kan 'yan Afirka

Manchester City ta sayi ɗan wasan Masar, Omar Marmoush, daga Eintracht Frankfurt kan dala miliyan 87, sannan ta kuma ɗauki ɗan Ghana, Antoine Semenyo, daga Bournemouth kan dala miliyan 83.

Kara karanta wannan

Dara ta ci gida: Wani bam ya fashe da ƴan ƙungiyar ISWAP yayin da suke hada shi

Manchester United ma ta shiga cikin manyan cinikai bayan ta sayi ɗan Kamaru Bryan Mbeumo daga Brentford kan dala miliyan 87.

Paris Saint-Germain ta ɗauki Achraf Hakimi daga Inter Milan kan dala miliyan 78, yayin da Manchester City ta sayi Riyad Mahrez daga Leicester City kan adadin kuɗi iri ɗaya.

Ɗan wasan Ghana, Mohammed Kudus, ya koma Tottenham Hotspur daga West Ham United kan dala miliyan 74, yayin da Pierre-Emerick Aubameyang ya kammala jerin da ciniki mai darajar dala miliyan 74.

Jerin 'yan kwallon Afirka mafi tsadar ciniki

A cewar rahoton Bleacher Report, waɗannan su ne manyan 'yan wasan Afirka mafi tsadar ciniki a tarihi:

Victor Osimhen ya shiga jerin 'yan wasan Afrika mafi tsada har a wuri biyu
Fitaccen dan wasan gaban Najeriya, Victor Osimhen da yanzu yake taka leda a Galatasaray. Hoto: Abdulhamid Hosbas/Anadolu via Getty Images
Source: Getty Images
  • Yan Diomande – RB Leipzig zuwa Real Madrid – dala miliyan 144
  • Nicolas Pépé – Lille zuwa Arsenal – dala miliyan 92
  • Victor Osimhen – Lille zuwa Napoli – dala miliyan 91
  • Omar Marmoush – Eintracht Frankfurt zuwa Manchester City – dala miliyan 87
  • Bryan Mbeumo – Brentford zuwa Manchester United – dala miliyan 87
  • Victor Osimhen – Napoli zuwa Galatasaray – dala miliyan 87
  • Antoine Semenyo – Bournemouth zuwa Manchester City – dala miliyan 83
  • Achraf Hakimi – Inter Milan zuwa PSG – dala miliyan 78
  • Riyad Mahrez – Leicester City zuwa Manchester City – dala miliyan 78
  • Mohammed Kudus – West Ham United zuwa Tottenham – dala miliyan 74
  • Pierre-Emerick Aubameyang – dala miliyan 74

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah ta dakatar da wani babban biki a Yobe, an cafke ɗan TikTok a Kano

Rahoton ya nuna yadda ƙimar 'yan wasan Afirka ke ci gaba da ƙaruwa a kasuwar cinikayyar ƙwallon ƙafa, yayin da manyan ƙungiyoyin Turai ke ci gaba da zuba jari mai yawa domin samun ƙwararrun 'yan wasa daga nahiyar.

Marsandi ya kai karar Osimhen

A wani labari, mun ruwaito cewa, kamfanin Mercedes-Benz, ya shigar da ƙara gaban 'yan sandan Italiya kan ɗan wasan Najeriya, Victor Osimhen.

Ana zargin ɗan wasan mai shekaru 27 da gazawa wajen biyan sauran kuɗaɗen motar da ya yi hayarta tun a 2023, inda bashin ya kai €90,000.

Rahotanni sun nuna cewa Osimhen bai kammala biyan kuɗin motar ba, sannan kuma bai mayar da ita ga kamfanin Marsandi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com