Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranar hutu domin murnar zagayowar ranar dimokuradiyya. Za a yi hutun ne domin tunawa da mulkin dimokuradiyya.
Majalisar dattawan Najeriya ta amince cewa kwamitin kula da asusun gwamnati ya wuce gona da iri a bincike yadda aka yi da N210trn a NNPCL karkashin Mele Kyari.
Tsohon mataimakin darakta a hukumar tsaron farin kaya ta kasa (DSS), Dennis Amachree, ya yi bayani filla-filla kan mutuwar marigayi Janar Sani Abacha.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin da ya jawo sanadiyyar kashe 'yan sa-kai a jihar Plateau. Mutanen yankin sun shiga alhini da fargabar kisan.
Majalisar wakilai ta amince da kudirin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi a Najeriya bayan ‘yan majalisa 288 sun kada kuri'ar goyon bayan wannan kudiri.
Hon. Fred Agbedi ya zama sabon shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilan Najeriya bayan murabus din Kingsley Chinda domin takarar gwamnan APC.
Wata mota dauke da fasinjoji ta taka wani bam da ake zargin 'yan bindiga ne suka dasa shi a jihar Zamfara. Mutane sun rasu yayin da wasu suka jikkata.
Tsohon shugaban kamfanin NNPCL, Malam Mele Kyari ya musamta kin amsa gayyatar kwamitin majlisar dattawa kan binciken da suke yi kan badakalar kudi.
Kwamitin majalisar Dajalisar dattawa kan asusun jama'a, ya gudanar da zama a ranar Laraba, 10 ga watan Yunin 2026. Ya cimma matsayar a cafke Mele Kyari.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari