Majalisar Dattawa Ta Kunyata Sanata kan Umarnin Kama Tsohon Shugaban NNPCL, Mele Kyari
- Majalisar Dattawa ta musanta ba da sammacin kama tsohon shugaban kamfanin mai na Najeriya, NNPCL, Mele Kyari
- Sanatoci sun bayyana cewa shugaban majalisa ne kaɗai ke da iko da karfin fitar da irin wannan sammaci a hukumance
- Majalisar ta ce kwamitin kula da asusun gwamnatin Najeriya ya wuce iyakarsa, ta kuma nesanta kanta da kalaman Adams Oshiomhole
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar Dattawa ta ce ba ta amince da sammacin kama tsohon Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), Mele Kyari, wanda Kwamitin Kula da Asusun gwamnati ya fitar ba.
Lamarin ya taso ne a zaman majalisar na yau Alhamis, bayan shugaban masu rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele, ya gabatar da batun karkashin dokokin majalisa.

Source: Facebook
Majalisa ta soke sammacin kama Mele Kyari
A rahoton The Cable, Bamidele jaddada cewa doka ta bai wa shugaban majalisar dattawa kaɗai ikon fitar da sammaci domin tilasta wa wani shaida halartar zaman majalisa ko na kwamitocinta.
Bayan tattaunawa, sanatocin sun yanke shawarar cewa sammacin da kwamitin ya fitar bai dace da doka ba saboda kwamitin ya wuce gona da iri.
Majalisar ta kuma umurci dukkan kwamitocinta da su bi kundin tsarin mulki, dokokin majalisa da ka'idojin aikinsu yayin gudanar da bincike da sa ido.
Majalisar dattawa ta yi fatali da kalaman Oshiomhole
Majalisar ta kuma bayyana cewa kalaman da aka danganta wa Sanata Adams Oshiomhole na cewa NNPCL "gungu ne na barayi da masu laifi" ba daga gare ta suka fito ba.
Sanatoci sun ce dole ne a mutunta ka'idar sauraron ɓangarorin biyu, adalci da kuma rashin yanke hukunci kafin kotu ta yanke.
Barau da wasu sanatoci sun yi martani
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ce kwamitin ya yi kuskure a matakin da ya dauka kan Mele Kyari.
"Fitar da sammaci aiki ne na shugaban majalisa. Kwamitin ya wuce iyakarsa," in ji Barau.
Shi ma babban mai tsawatarwa na majalisa, Sanata Tahir Monguno, ya ce dole ne majalisa ta kasance abin koyi wajen bin doka.
Sanata Orji Uzor Kalu da Sanata Adamu Aliero sun bukaci Oshiomhole ya janye kalamansa kan NNPCL.
Sanata Oshiomhole ya kare kansa
Da aka ba shi damar magana, Oshiomhole ya ce furucin nasa ya fito ne bayan wani tsohon jami'in kudi na NNPCL ya yi kalaman da ya dauka a matsayin cin zarafin sanatoci.
Ya amince cewa ya yi magana cikin fushi, amma ya ce manufarsa ita ce kare martabar majalisar dattawa, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan ya ce:
"Na yi magana ne cikin fushi, amma akwai masu gudanarwa nagari da yawa a NNPCL."
Ya kara da cewa bai yi niyyar bata sunan dukkan ma'aikatan kamfanin ba, sai dai ya mayar da martani ne ga abin da ya faru a zaman kwamitin.
Mele Kyari ya maida martani
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kamfanin mai na kasa (NNPCL), Malam Mele Kyari, ya ce ya yi mamakin sammacin kama shi da kwamitin Majalisar Dattawa ya fitar.
Ya musanta zargin cewa ya yi biris da gayyatar Majalisar Dattawa, inda ya ce bai ga wata sabuwar gayyata daga kwamitin ba kafin a bada sammacin kama shi.
Malam Mele Kyari ya bayyana cewa yanayin lafiyarsa a halin yanzu ne ya hana shi damar halartar zaman kwamitin kai tsaye.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

