Rahoto Ya Nuna Mutumin da Atiku Zai Dauka Mataimaki a Zaben 2027
- Atiku Abubakar ya zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara a Najeriya
- Alamu sun nuna cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya zabi abokin takararsa domin karawa da Shugaba Tinubu a 2027
- Idan ba wani canji aka samu ba, Atiku zai yi takara tare da daya daga cikin mutanen da suka fafata a zaben fitar da gwani na jam'iyyar ADC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Alamu sun nuna Atiku Abubakar ya zabi wanda zai yi masa mataimaki a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Idan ba wani canji aka samu ba, Atiku Abubakar ya yi nasarar kafa yiwuwar tikitin ‘AA’ a takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, ta hanyar zaɓar tsohon Ministan sufuri, Chibuike Amaechi, a matsayin abokin takararsa.

Kara karanta wannan
"Duk shiri ne," Babachir Lawal ya sake tabo yadda ADC ta tsaida Atiku takara a zaben 2027

Source: Twitter
Jaridar The Guardian ta kawo rahoton yiwuwar zabin da Atiku zai yi na dan takarar mataimakin shugaban kasa a ranar Juma'a, 12 ga watan Yunin 2026.
Amaechi na iya zama abokin takarar Atiku
Wannan mataki da ya zo bayan makonni na tsauraran tattaunawa a cikin dandalin haɗin gwiwa na ADC wanda ya fuskanci rigima bayan zaɓen fitar da gwani.
Zaɓen Amaechi ya zo ne a matsayin wani babban mataki na tinkarar tikitin 'OK' da ya haɗa Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a jam'iyyar hamayya ta NDC domin zaɓen shugaban ƙasa na ranar 16 ga watan Janairu, 2027.
Ta hanyar amincewa da Amaechi, Atiku da alama ya yanke shawarar yin abin da ya gaza yi a lokacin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2023, lokacin da ya ƙi amincewa da Nyesom Wike, wanda sya zo na biyu a zaɓen fitar da gwani na PDP.

Kara karanta wannan
Lokuta 6 da Atiku ya nemi samun kujerar shugaban kasa da yadda takarar ta kasance
Na kusa da Amaechi ya yi magana
Wani na kusa da Amaechi ya sanar da jaridar cewa tsohon Ministan sufurin ya amince bayan matsin lamba da roƙo daga manyan shugabannin siyasa daga shiyyar Arewa-maso-Yamma da Kudu-maso-Kudu.
Ya ce Atiku ya ba da tabbacin cewa:
"Wanda aka zaɓa a matsayin dan takarar mataimakin shugaban ƙasa zai samu manyan ayyuka da zai gudanar a lokacin kamfen da kuma a gwamnati”.

Source: Facebook
Jigon ADC ya yi karin haske
Kafin hakan jigon ADC, Eze Chukwuemeka Eze, ya yi watsi da kalaman da aka danganta ga Dele Momodu, waɗanda ke nuna cewa Amaechi ya ƙi karɓar gurbin mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar gabanin babban zaɓen 2027.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 11 ga watan Yunin 2026, Eze ya bayyana kalaman Momodu a matsayin ra'ayi na kashin kansa wanda zai iya haifar da fargaba, rashin yarda da juna, da rashin fahimtar juna a cikin jam'iyyar.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta tsorata, ta ce Peter Obi zai iya ba Atiku mamaki a zaben 2027
A cewarsa, kalaman Amaechi bayan zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na ADC sun nuna cewa babu wani mutum da ya tuntuɓe shi game da batun matsayin dan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Atiku ya yi wa Babachir martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya maida martani ga kalaman Babachir David Lawal.
Atiku ya zargi Babachir da yin kalamai da ka iya rusa hadin kan da ke tsakanin 'yan Najeriya da kuma nuna bambancin kabila.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa abin da ya fi damunsa shi ne yadda Babachir ke kokarin alakanta wata kabila baki daya da aikata laifuffuka.
Asali: Legit.ng