'Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Tsaron da Ke Kare Mutane a Plateau
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun sake kai harin da ya yi sanadiyyar hallaka jami'an tsaro na 'yan sa-kai a jihar Plateau
- Hatsabiban 'yan bindigan sun hallaka 'yan sa-kan ne yayin da suka kai wani hari cikin dare a karamar hukumar Riyom ta jihar
- Mutanen garin da aka kai harin, sun bayyana jami'an tsaron da aka kashe a matsayin jajirtattu wadanda suka sadaukar da ransu don kare al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - 'Yan bindiga masu ɗauke da makamai sun kashe jami'an tsaro na 'yan sa-kai guda biyu a jihar Plateau.
'Yan bindigan sun kashe jami'an tsaron na 'yan sa-kai ne a garin Ta-Hoss da ke karamar hukumar Riyom ta jihar Plateau.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce mazauna garin sun sun ce an farmaki mutanen ne da misalin ƙarfe 10:00 na daren ranar Laraba, 10 ga watan Yunin 2026, lokacin da suke gudanar da aikin gadi domin tsaron al'ummarsu.
'Yan bindiga sun kashe 'yan sa-kai
An gano sunayen mamatan da aka kashe da Davou Dalyop Patu, mai shekaru 48, da Dalyop Zaram, mai shekaru 38, kuma duka an bayyana su a matsayin mambobi masu jajircewa a ƙungiyar sa-kai da ke sadaukar da kai don kare garin.
Kisan dakarun na sa-kai guda biyu ya tsananta fargaba a yankin, inda mazauna garin ke nuna fargaba game da ci gaban ƙalubalen tsaro da ke fuskantar al'ummomin karkara a karamar hukumar Riyom, rahoton Vanguard ya nuna hakan.
Mutane sun shiga jimami a Plateau
Wani shugaban al'umma, Livinus Badung, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya koka game da harin har ya bayyana mamatan a matsayin mutane masu kishin kasa waɗanda suka sadaukar da lokacinsu da ƙarfinsu domin tabbatar da tsaron mutanensu.
A cewarsa, mutuwar tasu ta bar mutane cikin tsananin kaɗuwa yayin da mazauna garin ke jimamin dakarunsu na sa-kai guda biyu masu sadaukar da kai don samar da tsaro.

Kara karanta wannan
An shiga firgici da 'yan bindiga suka kai hari a Sokoto, an kashe jami'in tsaro da sace mutane

Source: Original
An koka kan rashin tsaro
Haka kuma yayin da yake tabbatar da lamarin, sakataren yaɗa labarai na kasa na kungiyar matasan Berom (BYM), Rwang Tengwong, ya bayyana alhininsa sannan ya mika saƙon ta'aziyya ga iyalan da abin ya shafa da kuma mutanen garin Ta-Hoss.
Tengwong ya koka kan ci gaba da kai hare-hare a kan garuruwan da ke fuskantar barazana, sannan ya yi kira ga hukumomin tsaro da su tsananta ƙoƙari don kare rayuka da dukiyoyi.
Hakazalika, ya buƙaci hukumomi da su tabbatar da cewa an gano waɗanda suka kai harin kuma an gurfanar da su gaban shari'a.
'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an 'yan sanda sun samu nasarar hallaka wasu 'yan bindiga bayan sun yi arangama a Abuja.
'Yan sanda sun harbe akalla mambobi biyu na ƙungiyar 'yan bindiga ne ke addabar mazauna babban birnin tarayya Abuja har lahira.
Kwamishinan 'yan sanda na Abuja, Ahmed Mohammed Sanusi ya ce shi da kansa ya jagoranci aikin da ya yi sanadiyyar mutuwar hatsabiban 'yan bindigan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng