Dan Majalisar Tarayya da Ya Yi wa Obi Shagube kan Zabe Ya Sha Ihun ‘Ba Mu Yi’
- Wani ɗan majalisar wakilai ya fuskanci rashin amincewar wasu daga mazaɓarsa yayin wani taron siyasa
- Dan siyasar ya sha bayyana cewa Peter Obi ba zai iya lashe zaɓen 2027 ba, har ma ya ce ba zai ci rumfarsa ba
- Shugaban APC Emmanuel Enoidem ya nemi a sake zaɓen shi, yayin da ɗan majalisar ya ce masu zaɓe ne ke da ikon yanke hukunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Uyo, Akwai Ibom - Wani ɗan majalisar wakilai, Clement Jimbo, wanda ya ke yawan cewa Peter Obi ba zai ci zabe ba.
Dan siyasar ya fuskanci matsala daga yan mazabarsa inda suka yi ta masa ihun bama yi saboda yawan suka ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi.

Source: Facebook
An bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin wani taron siyasa da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Etim Ekpo da ke Akwa Ibom, cewar Premium Times.
Yadda Jimbo ke yawan taba Obi
Jimbo na wakiltar mazaɓar tarayya ta Abak/Etim Ekpo/Ika ne a ƙarƙashin jam’iyyar APC, kuma yana neman wa’adi na biyu a majalisar a zaɓen 2027.
Ɗan majalisar ya bayyana aƙalla a hirarraki biyu da aka yi da shi tsakanin Janairu da Fabrairu cewa Obi “yana tafiya ne sabanin hanyar samun nasarar kowane zaɓe a ƙasar nan.”
A watan Janairu, Jimbo ya ce a wata hira cewa Obi ba zai taɓa lashe zaɓen 2027 ba saboda shi “ba mai kishin ƙasa ba ne,” maimakon ya gabatar da “adawa mai ma’ana.”
Ya kuma zargi Obi da kasancewa yana nuna ƙasar cikin mummunan yanayi a lokuta daban-daban.
Bayan wata guda, a wata hira da TheCable, Jimbo ya ce, “Peter Obi hayaniya kawai yake yi. Ba zai iya lashe kowane zaɓe a Najeriya ba.”
Da aka tambaye shi musamman game da rumfar zaɓen Obi, Jimbo ya ce, “Ba zai ci rumfar zaɓensa ba, ku riƙe maganata.”

Kara karanta wannan
Pantami na murnar samun tikitin PDP, abokin hamayyarsa ya sha alwashin jawo masa matsala
Sai dai a ranar Alhamis, 24 ga Satumba, makomar siyasar Jimbo ta fuskanci abin da ya bayyana a matsayin turjiya, lokacin da jigo a APC na Akwa Ibom, Emmanuel Enoidem, ya nemi mazauna yankin su goyi bayan sake zaɓen ɗan majalisar.
A wurin taron, Enoidem ya yi kira ga mahalarta da su goyi bayan sake zaɓen Jimbo.
“Zai zama tawaye idan ba ku zaɓi dukkan ’yan takarar APC ba, kuma Clement Jimbo yana cikinsu, za mu dawo da shi ko kuna so ko ba ku so.
“Ba za mu ji tsoron ambaton Clement Jimbo ba. Za mu ambaci sunansa sau da yawa har sai sunan ya zama wani ɓangare na ku.”
Enoidem ya tsaya takarar kujerar Sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma a 2023, inda Godswill Akpabio ya yi nasara, daga baya ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.
A lokacin taron, yayin da kyamara ta karkata zuwa ga mahalarta, an ga wasu suna daga hannayensu, abin da ya nuna rashin amincewa da ƙoƙarin Enoidem na neman goyon bayan Jimbo.

Source: Twitter
Hasashen Jimbo kan Peter Obi a zabe
A hirar da aka yi da Jimbo a watan Fabrairu, ya yi watsi da ƙarfin siyasar Obi, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour a 2023, kafin daga baya ya koma ADC.
Jimbo ya ce Peter Obi ya rika sauya jam’iyyu ba tare da gina isasshiyar hanyar siyasa mai ƙarfi ba.
“Peter Obi hayaniya kawai yake yi. Ba zai iya lashe kowane zaɓe a Najeriya ba."
- In ji shi.
An gargadi yan Arewa kan zaben Obi
Mun ba ku labarin cewa shugaban APC Nentawe Yilwatda ya ce nasarar Atiku Abubakar ko Peter Obi a 2027 ka iya lalata Arewacin Najeriya baki daya.
Yilwatda ya kare cire tallafin man fetur, yana mai cewa kudaden da aka samu na taimakawa ayyukan hanyoyi, noma da ilimi a Arewa.
Asali: Legit.ng

