Lambar Su Pantami Ta Fito, INEC Za Ta Dauki Mataki kan 'Yan Takarar da Suka Karya Dokar Zabe
- INEC na duba hukuncin Kotun Ƙoli na 24 ga Satumba domin tantance matakin da za ta ɗauka kan ’yan takarar da hukuncin ka iya shafar su
- Wasu ’yan takara na ganin INEC ba za ta iya ɗaukar mataki a kansu ba har sai Kotun Ƙoli ta yi hukunci kai tsaye kan matsayarsu
- Ƙarancin lokaci kafin fitar da jerin sunayen ƙarshe ya sa INEC ke ƙoƙarin samun kwafin hukuncin da aka tabbatar domin sashen shari’arta ya nazarce shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Alamu sun nuna cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) na duba yiwuwar ɗaukar mataki kan ’yan takarar da ake zargin sun karya wasu tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026, sakamakon hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke.
Wasu daga cikin ’yan takarar da suka samu tikiti bayan wasu zaɓukan fitar da gwani masu cike da ce-ce-ku-ce na ganin cewa, tun da Kotun Ƙoli ba ta ambaci sunan wani ɗan takara kai tsaye ba, INEC ba za ta iya ɗaukar mataki a kansu ba.

Kara karanta wannan
Akwai kura: Shugaban APC ya hango matsalar da Arewa za ta shiga idan Tinubu bai zarce ba

Source: Facebook
INEC na fuskantar matsin lokacin fitar da jerin sunaye
Wata majiya mai inganci a INEC ta tabbatar wa jaridar Daily Trust cewa hukumar na cikin damuwa saboda fargabar da hukuncin ya haifar da kuma fassarori daban-daban da ake yi masa.
Majiyar ta ce INEC na iya ɗaukar matakan da suka dace da zarar sashen shari’arta ya tabbatar da cewa doka ta ba ta damar yin hakan.
Karancin lokacin da ya rage kafin INEC ta fitar da jerin sunayen ’yan takara na ƙarshe na iya hana hukumar jiran sakamakon wasu sababbin kararraki kafin ta yanke hukunci.
Lokacin da INEC za ta fitar da jerin sunayen ƙarshe
Tsarin jadawalin zaɓen da INEC ta fitar ya tanadi cewa za a wallafa jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya kafin ko zuwa 12 ga Satumba.
Haka kuma, an tsara fitar da jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar gwamna da Majalisar Dokokin Jihohi zuwa 10 ga Oktoba 2026.
Majiyoyin cikin hukumar sun ce saboda ƙarancin lokaci, ana sa ran INEC za ta bayyana matsayinta kan batun a mako mai zuwa.
Hukumar kuma na ƙoƙarin samun Certified True Copy (CTC), wato kwafin hukuncin Kotun Ƙoli da aka tabbatar, domin sashen shari’arta ya fara nazarin hukuncin.
Mohammed Haruna ya tabbatar da nazarin hukuncin
Da aka tuntubi Kwamishinan INEC na Ƙasa mai kula da Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe, Malam Mohammed Haruna, ya tabbatar cewa hukumar na shirin nazarin hukuncin bayan samun CTC.
Haruna ya ce a al’ada, samun kwafin hukuncin da aka tabbatar na iya ɗaukar kusan mako guda. Sai dai ya ce hukuncin da ake magana a kai an yanke shi ne ranar 24 ga Satumba, wanda bai kai mako guda ba a lokacin da aka tuntube shi.
Ya ce da zarar hukumar ta samu hukuncin, sashen shari’a zai fara aiki a kansa, sannan kwamishinonin hukumar su gudanar da taro domin yanke matsayar INEC kan batun.
Fargaba kan makomar wasu ’yan takara
Haruna ya kuma tabbatar da cewa akwai batutuwa da dama da ke bukatar warwarewa dangane da hukuncin, lamarin da ya haifar da fargaba tsakanin hukumar da jam’iyyun siyasa.
Ya ce babu tabbas a halin yanzu kan makomar ’yan takarar da ake ganin za su iya shiga cikin wadanda hukuncin zai shafa.
Daga cikin sunayen da ake nuna fargabar za su iya fuskantar matsala akwai tsohon Sufeto-Janar na ’Yan sanda, Mohammed Adamu; Sheikh Isa Pantami; Kingsley Chinda; Shehu Buba da Mohammed Nami.

Source: Facebook
Pantami ya lashe zaben fitar da gwani
A wani labarin kuma, kun ji cewa Farfesa Isa Ali Pantami, ya zama ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar Gombe na 2027.
Farfesa Pantami ya zama halastaccen dan takarar PDP ne bayan kammala tattara sakamakon zaben fitar da gwani daga ƙananan hukumomi 11 na jihar Gombe.
Asali: Legit.ng

