Omar Artan: Alkalin Wasan da Amurka ta Hana Hura Gasar Kofin Duniya Ya Samu Dama a Wurin UEFA

Omar Artan: Alkalin Wasan da Amurka ta Hana Hura Gasar Kofin Duniya Ya Samu Dama a Wurin UEFA

  • Hukumar kwallo kafa ta Turai (UEFA) ta tuna da alkalin wasa, Omar Artan, da Amurka ta hana shiga kasarta don hura gasar cin kofin duniya
  • UEFA ta yaba da hazaka da kwarewar aikin Omar Artan wanda Amurka ta hana samun damar hura wasa a gasar cin kofin duniya ta 2026
  • Hukumar UEFA ta zabi Omar Artan a matsayin wanda zai zama alkalin wasa a gasar cin kofin Super Cup da za a gudanar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Tarayyar Turai - Hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai (UEFA) ta zabi Omar Artan, alƙalin wasa ɗan ƙasar Somaliya wanda aka hana shiga ƙasar Amurka, don hura mata wasa.

UEFA ta zabi Omar Artan wanda daga baya aka cire shi daga cikin rukunin alƙalan wasa na gasar cin kofin duniya na 2026, domin ya jagoranci wasan kofin UEFA Super Cup na kakar wasa mai zuwa.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Amurka ta jefa makamai, an hallaka jami'an kasar Indiya

Omar Artan zai hura wasan gasar UEFA Super Cup
Omar Artan na hura wasan Gabon da Ivory Coast a gasar AFCON 2025 Hoto: NurPhoto
Source: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton zabin da hukumar UEFA ta yi wa Omar Artan a ranar Alhamis, 11 ga watan Yunin 2026.

UEFA ta ba Artan jagorancin wasa

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai ta sanar da cewa Artan ne zai jagoranci fafatawa tsakanin Paris Saint-Germain, zakarun gasar UEFA Champions League, da kuma Aston Villa F.C., zakarun gasar UEFA Europa League.

An shirya gudanar da wasan ne na lashe kofin UEFA Super Cup a ranar 12 ga watan Agustan 2026 a birnin Salzburg.

Hukumar UEFA ta ce naɗin ya biyo bayan tattaunawa da aka yi da hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF), tashar Channels tv ta kawo rahoton.

UEFA ta yaba da kwazon Omar Artan

Shugaban UEFA, Aleksander Čeferin, ya ce “hazaka da ƙwarewar aikin alƙalanci” na Omar Artan sun sa ya cancanci wannan gagarumin aiki.

“Omar Artan babban alƙalin wasa ne matashi amma kuma gogagge, wanda ya nuna ƙwarewarsa a matakin gasa mafi girma na hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka."

Kara karanta wannan

"Za su dandana kudarsu"; Trump ya yi sabuwar barazana ga Iran bayan musayar hare hare

- Alexsander Ceferin

Ya ƙara da cewa an samar da ƙwallon ƙafa ne domin haɗa kan mutane, kuma shawarar UEFA tana nuna girmamawa ga iyawar Artan.

Alexsander Ceferin ya kuma gode wa shugaba CAF, Patrice Motsepe, saboda goyon bayan wannan mataki.

Omar Artan zai hurawa UEFA wasa
Alkalin wasa, Omar Artan, yayin wasan Ivory Coast da Gabon a gasar AFCON 2025 Hoto: NurPhoto
Source: Getty Images

Amurka ta hana Artan shiga kasar

Omar Artan yana cikin alƙalan wasa 52 da FIFA ta zaɓa domin jagorantar wasanni a gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2026.

Sai dai, bayan isarsa filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Miami, hukumomin Amurka sun hana shi shiga ƙasar, inda aka ruwaito suna iƙirarin cewa yana “da alaƙa da mambobin ƙungiyoyin ta'addanci da ake zargi,” wanda hakan ya sa bai cancanci shiga ƙasar ba.

'Yan wasan Iran za su shiga Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan wasan tawagar kwallon kafa ta Iran sun samu bizar shiga kasar Amurka domin fafatawa a gasar cin kofin duniya.

Kara karanta wannan

Kofin duniya: Trump ya yi wa tawagar 'yan kwallon Iran rashin mutunci a Amurka

Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya nuna cewa gwamnatin Trump ba ta da wata matsala wajen bayar da bizar ga tawagar Iran.

Tawagar Iran za ta buga wasanninta a Amurka amma ana sa ran za ta zauna a Mexico saboda wasu matsaloli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng