Mele Kyari: Kwamitin Majalisa Ya Umarci Cafke Tsohon Shugaban NNPCL
- Lambar tsohon Shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari, don neman bayanai kan yadda aka yi da wasu kudaden da suka kai N210trn
- Kwamitin Majalisar dattawa kan asusun jama'a ya gaji da jiran bayyanar Mele Kyari a gabansa, don haka ya umarci a cafke shi
- Wasu sanatoci sun bukaci a karawa Mele Kyari lokaci inda suka yi nuni da cewa tsohon shugaban na NNPCL bai da lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kwamitin Majalisar Dattawa kan asusun jama'a ya bayar da umarnin kama tsohon shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Mele Kyari.
Kwamitin ya ba da umarnin kama Mele Kyari ne saboda gaza bayyana a gabansa kan zarge-zargen da suka shafi kuɗaɗe har Naira tiriliyan 210 waɗanda ba a bayyana yadda aka yi da su ba tsakanin shekarar 2017 da 2023.

Kara karanta wannan
"Sau 3 kacal na ga ƴaƴana," Zulum ya tuno abin da ya faru da shi bayan zaben 2019

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa kwamitin ya bayar da umarnin ne a ranar Laraba, 10 ga watan Yunin 2026.
Meyasa aka yi umarni cafke Mele Kyari?
Wannan umarni ya biyo bayan rashin halartar Kyari akai-akai a wajen taron binciken da ake gudanarwa kan wasu tambayoyi da ofishin babban akanta janar na tarayya ya tayar game da bayanan kuɗaɗen kamfanin a tsawon lokacin da ake bincika.
Sai dai, tsohon babban jami'in kuɗi na NNPCL, Umar Isa, ya ƙalubalanci zarge-zargen a gaban kwamitin, inda ya jaddada cewa babu wasu kuɗaɗe da suka ɓata.
Sannan ya bayyana adadin Naira tiriliyan 210 ɗin a matsayin mai rudarwa idan aka kwatanta shi da ainihin abin da kamfanin ya samu a tsawon wannan lokacin.
An fitar da umarnin kama Mele Kyari ne bayan da 'yan majalisar suka yanke hukuncin kin ci gaba da jinkirta binciken.
An bukaci a yi wa Mele Kyari uzuri
A lokacin zaman, Sanatoci Saliu Mustapha (Kwara ta Tsakiya) da Tony Nwoye (Anambra ta Arewa) sun yi kira da a bi abin a hankali, suka buƙaci kwamitin ya sake ba wa Kyari wata damar na bayyana a gabansa.
Sun yi nuni da cewa rahotanni sun nuna yana fama da rashin lafiya kuma yana karɓar magani a ƙasar Jamus, jaridar TheCable ta kawo labarin.
Amma sauran mambobin kwamitin sun nuna tsananin adawa ga wannan roƙo na su, suka jaddada cewa dole ne binciken ya ci gaba ba tare da ƙarin jinkiri ba, sannan suka buƙaci a fitar da takardar umarnin kama shi.
Sanata Abdul Ningi (Bauchi ta Tsakiya) ya bayyana cewa bai kamata a karɓi bayanan uzuri na baki ba tare da kwararan hujjoji na takarda da ke nuna rashin lafiya ba, matsayin da daga bisani Sanata Victor Umeh (Anambra ta Tsakiya) ya goyi baya, wanda shi ne ma ya gabatar da kudirin neman kama Kyari a hukumance.

Source: Facebook
Sanatoci sun amince a cafke Mele Kyari
Tsohon gwamnan jihar Edo kuma sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, shi ma ya bayyana cewa Majalisar Dattawa na fuskantar barazanar rage darajar ikonta idan ta gaza tilasta bin sammacin da take bayarwa.
Bayan jefa ƙuri'ar muryoyi, shugaban kwamitin, Sanata Ibrahim Dankwambo (Gombe ta Arewa), ya yanke hukuncin cewa a kamo Kyari kuma a gabatar da shi a gaban kwamitin.
“Duk inda Mele Kyari yake, a kama shi a kawo shi gaban wannan kwamitin."
- Sanata Ibrahim Dankwambo
Mele Kyari ya je wurin EFCC
A wani labarin kuma, kunnji cewa tsohon shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari, ya kai kansa hedkwatar hukumar EFCC.
Mele Kyari wanda aka taba saka sunansa a jerin wadanda ake sa ido a kansu, ya je hukumar ne domin amsa tambayoyi.
Zai amsa tambayoyi ne kan yadda aka yi amfani da kudaden da aka ware, domin gyaran matatun mai a lokacin da yake rike da mukamin shugabancin kamfanin NNPCL.
Asali: Legit.ng

