Gwamna Radda Ya Sauya Matsaya kan Sulhu da 'Yan Bindiga a Katsina
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya aika sako ga 'yan bindigan da ke kai hare-hare kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba
- Dikko Radda ya bukaci 'yan bindigan da su ajiye makamansu domin rungumar zaman lafiya da daina aikata barna
- Gwamnan ya nuna cewa kofa a bude take ga duk wadanda suka rungumi zaman lafiya domin samun hanyar shiga cikin al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya janye matsayarsa ta baya na ƙin yin tattaunawa da 'yan bindiga da ke addabar al'ummomi a faɗin jihar.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa ƙofar tattaunawa a buɗe take ga waɗanda ke son rungumar zaman lafiya.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa gwamnan ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Yunin 2026, yayin buɗe wa da kuma miƙa rukunin gidaje 152 ga 'yan gudun hijira a karamar hukumar Jibia ta jihar.

Kara karanta wannan
'Nigeria Air': EFCC ta tona yadda Ministan Buhari ya yaudari 'yan kasa da jirgin aro
An gina gidajen ne a ƙarkashin aikin UNDP Northwest Prevention Facility Project tare da tallafin gwamnatin ƙasar Jamus da haɗin gwiwar gwamnatin jihar.
Me Radda ya ce kan tattaunawa da 'yan bindiga?
Gwamna Radda ya ce gwamnatin jihar tana nan a shirye don yin tattaunawa da 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane waɗanda suka yi watsi da ayyukan laifi da gaske.
Ya jaddada cewa gwamnatin jihar Katsina a shirye take ta sauƙaƙa musu hanyoyin sake shiga cikin al'umma.
Gwamnan ya buƙace su da su yi watsi da tashen hankula, su rungumi tattaunawa, sannan su miƙa makamansu domin maslahar zaman lafiya da ci gaba.
Gwamna Radda ya yi kira ga 'yan bindiga
Radda ya yi kira ga waɗanda har yanzu suke da hannu a ayyukan laifi da su tuba su koma ga iyalansu da al'ummominsu, inda ya tabbatar musu cewa tallafin gwamnati da damarmaki za su iya isa gare su idan suka zaɓi hanyar zaman lafiya ta hanyar ajiye makamansu.
“Zuwa ga 'yan uwanmu maza da mata da ke cikin daji, ga waɗanda har yanzu suke amfani makamai kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba."
"Da kuma waɗanda ke da hannu a ayyukan 'yan bindiga, garkuwa da mutane, da tashe-tashen hankula, ku saurare ni da kyau a yau: akwai hanya mafi kyau, ƙofofin tattaunawa, tuba, da sake karɓar ku a cikin al'umma a buɗe suke.”
“Ku ajiye makamanku ku koma ga iyalanku da al'ummominku. Irin waɗannan gidaje, tallafi, da damarmaki da ake samarwa a nan yau za su iya kasancewa naku a gobe."
"Ba ta hanyar tsoratarwa ko zubar da jini ba, amma ta hanyar zaman lafiya, kyakkyawan shugabanci, da halastaccen aiki. Ku zaɓi 'ya'yanku maimakon makamanku. Ku zaɓi ci gaba maimakon barna. Ku zaɓi rayuwa."
- Gwamna Dikko Umaru Radda

Source: Facebook
'Yan bindiga sun kashe 'yan sa-kai
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun yi ta'asa lokacin wani hari da suka kai a jihar Plateau.
'Yan bindigan sun kashe wasu jami'an tsaron na 'yan sa-kai guda biyu a garin Ta-Hoss da ke karamar hukumar Riyom ta jihar Plateau.
Mazauna garin sun sun ce an farmaki mutanen ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare, lokacin da suke gudanar da aikin gadi domin tsaron al'ummarsu.
Asali: Legit.ng
