A Karshe, Majalisa Ta Amince da Kudurin Dokar Kafa 'Yan Sandan Jihohi a Najeriya

A Karshe, Majalisa Ta Amince da Kudurin Dokar Kafa 'Yan Sandan Jihohi a Najeriya

  • Majalisar wakilai ta amince da kudirin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi bayan kuri’ar da ‘yan majalisa 288 suka kada a ranar Alhamis
  • Kudirin zai bai wa gwamnoni damar nada kwamishinonin ‘yan sanda tare da ba su umarni kan harkokin tsaro a matakin jihohinsu
  • Sai dai, dole ne Majalisar dattawa da majalisun jihohi su fara amince wa da wannan kuduri kafin rundunar ‘yan sandan jiha ta fara aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Majalisar wakilan Najeriya ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da zai bai wa jihohi damar kafa rundunar ‘yan sandan jiha domin yaki da matsalar tsaro da ke addabar kasar.

Kudirin wanda aka yi wa lakabi da “Kudurin gyaran kudin mulkin Najeriya na 1999 don bada damar kafa 'yan sandan jiha” ya samu amincewar 'yan majalisa ne yayin zaman yau karkashin jagorancin Tajudeen Abbas.

Kara karanta wannan

ESN ta shirya kai hare hare a wasu sassan Najeriya, DSS, sojoji sun dauki mataki

Majalisar wakilai ta amince da kudurin kafa 'yan sandan jihohi.
Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas yana jagorantar zaman majalisa a Abuja. Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

Majalisa ta amince da kafa 'yan sandan jihohi

Mataimakin shugaban majalisar kuma shugaban kwamitin gyaran kundin tsarin mulki, Benjamin Kalu, ne ya gabatar da hujjojin da suka goyi bayan kudirin tare da bukatar ‘yan majalisa su mara masa baya, kamar yadda Legit Hausa ta gani a shafin asusun NALTF.

An gudanar da kada kuri’ar ne ta hanyar daga hannu, inda kusan ‘yan majalisa 288 suka goyi bayan kudirin yayin da mutum hudu kacal suka nuna adawa da shi.

Kudirin na neman sauya tsarin aikin ‘yan sanda a Najeriya ta hanyar kafa rundunar ‘yan sandan tarayya da kuma ta jihohi.

Yadda tsarin 'yan sandan jihohi zai kasance

Sabon kudurin zai bai wa Majalisar tarayya damar tsara yadda rundunar ‘yan sandan tarayya za ta kasance tare da shimfida ka’idojin kafa ‘yan sandan jihohi.

Sai dai kudirin ya bayyana cewa babu wata rundunar ‘yan sandan jiha da za ta fara aiki sai Majalisar dokokin jihar ta amince da dokar kafa ta tare da tabbatar da ta cika sharudan kasa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 6 sun mutu yayin da suka yi yunkurin kai hari a jihar Zamfara

Haka kuma, rundunar ‘yan sandan tarayya za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a jihohin da ba su kafa rundunar ‘yan sandan jiha ba.

Tsoma bakin tarayya a tsaron jihohi

Kudirin ya takaita yadda Gwamnatin tarayya za ta rika tsoma baki cikin harkokin tsaron jihohi, a cewar rahoton jaridar Vanguard.

A karkashin tsarin, rundunar 'yan sandan tarayya za ta iya tsoma baki a harkokin jihohi ne kawai idan tsaro ya tabarbare gaba daya; idan gwamna ya bukaci taimako ko kuma idan rundunar jihar ta kasa gudanar da ayyukanta.

An kuma yi gyara kan tsarin nadin mukaman manyan jami’an ‘yan sanda.

A karkashin sabon tsarin, shugaban kasa ne zai nada sufeto janar na ‘yan sanda bisa shawarar majalisar kula da harkokin ‘yan sanda tare da amincewar Majalisar tarayya.

Hakazalika, gwamnoni ne za su nada kwamishinonin ‘yan sandan jihohi bisa shawarar majalisar kula da harkokin ‘yan sanda tare da amincewar majalisar dokokin jihar.

Kudurin kafa 'yan sandan jihohi zai ba gwamnoni ikon tafiyar da harkokin 'yan sandan jihohinsu.
Shugabannin rundunar 'yan sandan Najeriya bayan kammala wani taron bita a Abuja. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Gwamnoni za su ba 'yan sanda umarni

Kudirin ya bai wa gwamnoni damar bai wa kwamishinonin ‘yan sandan jihohi umarni kan harkokin tsaro da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun kashe babban soja da wasu sojoji 7 a Kaduna

Sai dai idan kwamishinan ya ga umarnin bai dace da doka ko ka’idojin aikin ‘yan sanda ba, zai iya kai batun gaban majalisar kula da harkokin ‘yan sanda domin yanke hukunci na karshe.

Duk da amincewar da majalisar wakilai ta yi, kudirin zai bukaci sahalewar majalisar dattawa da kuma amincewar akalla kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin jihohi kafin ya zama doka a hukumance.

Matsayar tarayya kan 'yan sandan jihohi

A wani labari, mun ruwaito cewa, tuni aka fara tattaunawa kan samar da tsarin ‘yan sandan jihohi bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu, kuma yanzu an kai matakin duba gyaran kundin tsarin mulki.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ne ya bayyana hakan bayan wani taron tattaunawa kan batun ‘yan sandan jihohi da aka shirya a Abuja.

Gbajabiamila ya bayyana cewa a halin yanzu hankalinsu yana kan gyaran kundin tsarin mulki, sannan daga baya za a samar da dokokin da za su ba tsarin damar aiki yadda ya kamata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com