Yadda Aka Yi Jigilar Sinadarin Hada Nukiliya a Asirce daga Venezuela zuwa Amurka

Yadda Aka Yi Jigilar Sinadarin Hada Nukiliya a Asirce daga Venezuela zuwa Amurka

  • Sojoji sun yi wa motar jigilar Uranium mai hatsari rakiya zuwa tashar jirgin ruwa domin kai wa Amurka cikin tsauraran matakan tsaro na musamman
  • Hukumar IAEA ta ce aikin kwashe Uranium ɗin haɗin gwiwa ne tsakanin Venezuela, Amurka da wasu hukumomin duniya masu kula tsaro
  • Masana sun bayyana cewa Uranium ɗin na iya zama barazana idan ya shiga hannun ƙasashe ko ƙungiyoyin da ke neman makaman nukiliya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - An gano yadda aka yi jigilar wani sinadarin Uranium mai matuƙar hatsari daga ƙasar Venezuela zuwa Amurka cikin tsananin sirri da tsaro.

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da aikin ne cikin dare a ƙarshen watan Afrilu, inda wasu motocin sojojin Venezuela suka raka wata mota daga cibiyar binciken kimiyya ta IVIC da ke kusa da Caracas zuwa tashar jiragen ruwa ta Puerto Cabello.

Kara karanta wannan

Dalibai sun tsere, iyaye sun kidime bayan jita jitar yan bindiga sun kutsa makarantu a Neja

Rahoto ya nuna cewa an kwashe Uranium daga Venezuela zuwa Amurka cikin sirri.
Direba na tuka motar da take kwashe baraguzan nukiliya a Fukushima da masana kimiyya rike da garwar sinadarin uranium. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

IAEA ta yi magana kan jigilar Uranium

Ana zargin motar na ɗauke da kusan kilogiram 13 na sinadarin Uranium da aka tace sosai, wanda aka fitar zuwa Amurka ƙarƙashin wani shiri na haɗin gwiwar ƙasashe da hukumomin duniya, cewar rahoton BBC Hausa.

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta tabbatar da aikin a wata sanarwa da ta fitar ranar 8 ga watan Mayu, tana mai cewa an tsara aikin cikin matakan tsaro masu tsauri domin kauce wa barazanar tsaro.

Masana sun bayyana cewa duk da ƙarancin adadin Uranium ɗin idan aka kwatanta da abin da ake zargin Iran ta mallaka, irin wannan sinadari na iya zama haɗari idan ya shiga hannun waɗanda ba su dace ba.

Ƙasashen duniya sun daɗe suna nuna damuwa kan kusancin Venezuela da ƙasashe irin su Iran da Rasha da Koriya ta Arewa, lamarin da ke sa Amurka da sauran ƙasashe sa ido sosai kan duk wata hulɗa da ta shafi makamashin nukiliya.

Kara karanta wannan

Iran ta rufe Hormuz gaba daya, ta farmaki jiragen da suka yi taurin kai

Abin da masana suka ce kan Uranium ɗin

Wani masani a cibiyar Royal United Services Institute, Jack Crawford, ya bayyana cewa kwashe Uranium daga Venezuela wani ɓangare ne na ƙoƙarin hana yaɗuwar sinadarin da za a iya amfani da shi wajen ƙera makaman nukiliya.

Ya ce duk da cewa Uranium ɗin bai kai matakin da ake amfani da shi kai tsaye wajen ƙera makami ba, akwai yiwuwar ƙara tace shi zuwa matakin da zai iya zama barazana.

Yadda Venezuela ta samu Uranium ɗin

Rahotanni sun nuna cewa asalin labarin ya samo tushe tun shekarar 1953, lokacin da tsohon shugaban Amurka Dwight Eisenhower ya gabatar da shirin “Atoms for Peace” a Majalisar Dinkin Duniya.

Shirin ya bai wa wasu ƙasashe damar amfani da fasahar nukiliya domin bincike da ayyukan zaman lafiya, ba tare da amfani da ita wajen ƙera makamai ba.

A ƙarƙashin wannan shiri ne Venezuela ta samu wata na’urar binciken makamashin nukiliya daga kamfanin General Electric na Amurka a shekarar 1960, kamar yadda aka wallafa a shafin hukumar IAEA.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Gwamna ya umarci rufe makarantu bayan samun rahoton DSS

An girke na’urar a cibiyar IVIC domin gudanar da bincike na kimiyya, kuma ta ci gaba da aiki har zuwa shekarun 1990 kafin a fara rufe ta sannu a hankali.

A 1953, shugaban Amurka na wancan lokacin ya gabatar da shirin 'Atoms for Peace' don kasashe masu sinadarin uranium.
Janar Arthur Summerfield (hagu) na mika daftarin shirin "Atoms for Peace" ga shugaban Amurka, Dwight D. Eisenhower a 1953. Hoto: Bettmann via Getty Images
Source: Getty Images

Me ya sa aka kwashe Uranium ɗin yanzu?

Hukumomin Venezuela sun ce an kwashe wani ɓangare na makamashin tun shekarar 1997, yayin da aka ci gaba da adana saurancikin tsaro.

Sai dai gwamnatin Birtaniya ta ce Venezuela ta nemi taimakon kwashe sauran Uranium ɗin tun a shekarar 2017, kuma daga baya aka fara shirye-shiryen gudanar da aikin.

Rahotanni sun ce sauye-sauyen siyasa a Venezuela, musamman bayan matsin lamba kan shugaba Nicolás Maduro, sun taimaka wajen gaggauta kammala aikin kafin lokacin da aka tsara da farko.

Iran za ta mika uranium ga Amurka

A wani labari, mun ruwaito cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta amince da wani shiri na musamman domin tabbatar da yarjejeniya da Amurka.

Iran ta amince ta mika tarin sinadarin uranium da aka tace sosai a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar da shugaban Amurka, Donald Trump.

Rahoton ya bayyana cewa adadin uranium ɗin da Iran ke da shi zai iya isa a ƙera bama-baman nukiliya guda 11 idan aka yi amfani da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com