Sojojin Sama Sun Jefe Bama Bamai a Mobayar 'Yan Ta'adda a Borno, an Kashe Kwamandoji
- Dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun ci gaba da kai hare-hare kan maboyar 'yan ta'adda a yankin Arewa maso Gabas
- Sojojin saman sun yi ruwan bama-bamai a wasu wuraren da 'yan ta'adda suke samun mafaka yankin Metele na jihar Borno
- Hare-haren da sojojin suka kai sun yi sanadiyyar hallaka 'yan ta'adda masu yawa tare da wasu manyan kwamandojinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Dakarun sojojin rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) sun kashe tarin 'yan ta'adda, ciki har da manyan kwamandojin da dama a Borno.
Dakarun sojojin sun kashe hatsabiban ne yayin da suka kai hare-haren sama a maboyar 'yan ta'adda a yankin Arewacin Tumbuns na tafkin Chadi.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce daraktan hulɗa da jama'a da yaɗa labarai na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya tabbatar da hakan ranar Alhamis, 11 ga watab Yunin 2026.
Daraktan yada labaran na rundunar sojojin saman ya ce an gudanar da hare-haren ne da safiyar ranar Laraba, 10 ga watan Yuni, 2026.
'Yan ta'adda na kai hare-hare
'Yan ta'adda sun sha kai wa dakarun Operation Hadin Kai da ke aiki a yankin kwantan ɓauna akai-akai kafin wannan samamen na baya-bayan nan na sojojin sama.
A makon da ya gabata, an ruwaito cewa 'yan ta'addan sun yi wa jami'an soja kwantan ɓauna a jihar Borno, inda suka kashe sojoji da dama sannan suka sare kan wasu daga cikin mamatan.
Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda
Aikin, wanda sashin dakarun saman na rundunar Operation Hadin Kai ya gudanar, ya farmaki sansanonin 'yan ta'adda da ke Metele, wani sanannen wurin buya na 'yan tawaye a jihar Borno.
A cewarsa, aikin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da kuma ayyukan bincike da sa ido na sirri, waɗanda suka tabbatar da kasancewar wani babban kwamandan 'yan ta'adda, maboyar 'yan ta'adda, da kuma ƙaruwar ayyukan 'yan tawaye a cikin yankin.
Yadda sojoji suka farmaki maboyar 'yan ta'adda
“Bisa ga aiki da bayanan sirrin, dakarun saman na NAF sun kai hari kan wuraren da aka gano cikin kwarewa. Bayan isarsu, ma'aikatan jirgin sun lura da gagarumar zirga-zirgar 'yan ta'adda a kewaye da gine-ginen da aka ɓoye, wanda hakan ya tabbatar da kasancewar miyagun mambobin.
“Bayan tantance wurin da kyau, jirgin ya ƙaddamar da munanan hare-hare a kan wuraren da aka ayyana."
"Tantance barnar yaƙi bayan harin ta tabbatar da lalata sansanin 'yan ta'addan da kuma kashe tarin dakarun 'yan ta'addan.”
- Ehimen Ejodame

Source: Original
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin sama na rundunar Operation Hadin kai sun hallaka 'yan ta'addan kungiyar ISWAP a jihar Borno.
Sojojin sun hallaka akalla 'yan ta'addan ISWAP guda tara bayan da suka yi ruwan bama-bamai daga sama kan maboyarsu.
Hakazalika, daarun sojojin sun lalata motoci da dama a lokacin hare-haren sama da aka kai a kewayen Cross Kauwa da Ali Sherifti da ke Arewacin jihar Borno.
Asali: Legit.ng

