An Zabi Sabon Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilan Najeriya

An Zabi Sabon Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilan Najeriya

  • An nada Hon. Fred Agbedi a matsayin sabon shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilan Najeriyan bayan murabus din Kingsley Chinda
  • Shugaban majalisa, Tajudeen Abbas ya ce 'yan bangaren marasa rinjaye sun cimma matsaya kan nade-naden shugabanninsu a majalisar
  • Sababbin nade-naden sun kawo karshen rikicin da ya ratsa cikin ‘yan adawa kan wanda zai maye gurbin tsohon shugaban marasa rinjayen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya sanar da nadin Hon. Fred Agbedi daga jihar Bayelsa a matsayin sabon shugaban marasa rinjaye na majalisar.

Tajudeen Abbas ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisa na ranar Alhamis, ya ce ‘yan bangaren marasa rinjaye sun cimma matsaya tare da amincewa da nadin Agbedi baki daya.

An zabi sababbin shugabannin bangaren marasa rinjaye na majalisar wakilan Najeriya.
Tajudeen Abbas yana jagorantar zaman majalisar wakilan Najeriya a Abuja. Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

Fred Agbedi ya zama shugaban marasa rinjaye

Kara karanta wannan

NNPCL: Mele Kyari ya aiko sako daga kasar waje bayan ba da umarnin kama shi

A cikin wasikar da kakakin majalisar ya karanta, bangaren marasa rinjaye ya bayyana cewa sun zabi Agbedi ne saboda gogewarsa da dadewar da ya yi a majalisar wakilai, kamar yadda rahoton The Nation ya nuna.

An bayyana cewa kujerar ta zama babu kowa ne bayan Hon. Kingsley Chinda ya yi murabus domin tsayawa takarar gwamnan jiha karkashin jam’iyyar APC.

Sauran shugabannin marasa rinjaye da aka sanar sun hada da Mansur Manu Soro daga jihar Bauchi wanda aka nada a matsayin bulalar marasa rinjaye.

Haka kuma, an nada Abdulsamad Dasuki daga jihar Sokoto a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye.

George Ozodinobi wanda ya rike mukamin shugaban marasa rinjaye na rikon kwarya bayan ficewar Chinda, ya koma matsayinsa na mataimakin bulalar marasa rinjayen.

Shugaban majalisa ya yi magana

Shugaban majalisar ya bayyana cewa da wannan nadin, an kammala cike dukkan mukaman shugabanci a majalisar wakilai.

Ya tabbatar da cewa shugabancin majalisar zai yi aiki tare da sababbin shugabannin marasa rinjayen domin tabbatar da nasarar manufofin majalisar ta 10.

“Ina taya sababbin shugabannin murna tare da yi masu fatan alheri a sababbin mukamansu. Za mu hada kai domin cimma manufofin wannan majalisa,” in ji Tajudeen.

Kara karanta wannan

Mele Kyari: Kwamitin majalisa ya umarci cafke tsohon shugaban NNPCL kan badakalar N210trn

Hon. Fred Agbedi ya zama sabon shugaban marasa rinajye na majalisar wakilan Najeriya
Hon. Fred Agbedi, mutumin da ya zama sabon shugaban marasa rinjaye na Majalisar wakilai. Hoto: @_Dejii
Source: Twitter

Rikici ya lafa a bangaren ‘yan adawa

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa ‘yan bangaren adawa sun nuna farin ciki bayan sanar da nade-naden, musamman bayan barazanar kaurace wa zaman majalisa idan ba a bayyana sunayen shugabanninsu ba.

Tun farko dai an yi rade-radin cewa Ikenga Ugochinyere ne zai maye gurbin Kingsley Chinda, amma batun ya jawo ce-ce-ku-ce da zargin amfani da sa hannun bogi.

Da wannan sabon ci gaba, bangarorin masu rinjaye da marasa rinjaye sun samu cikakken shugabanci a Majalisar wakilan Najeriya.

'Yan majalisa sun fice daga PDP

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya sake samun karuwa bayan ƴan majalisar wakilai sun bar PDP.

Makinde ya sake nuna tasirinsa a harkokin siyasa bayan mambobi na Majalisar Wakilai shida da ke biyayya gare shi sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APM.

Kakakin majalisar, Tajudeen Abbas, ya karanta wasiƙu 13 da ke sanar da sauya sheƙar ‘yan majalisa daga jam’iyya zuwa wata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com