Ranar Dimokuradiyya: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Lokacin Hutu

Ranar Dimokuradiyya: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Lokacin Hutu

  • Najeriya na shirin bikin cika shekara 27 da fara mulkin dimokuradiyya ba tare da katsewa ba tun daga shekarar 1999
  • Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, ta ayyana lokacin hutu ga ma'aikata domin murnar zagayowar ranar dimokuradiyya
  • Ministan harkokin cikin gida wanda ya fitar da sanarwar a madadin Gwamnatin tarayya, ya bukaci 'yan Najeriya su kasance masu bin doka da oda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma'a, 12 ga watan Yunin 2026 a matsayin ranar hutu ga dukkan ma'aikata.

Gwamnatin ta ba da hutun ne domin tunawa da cikar Najeriya shekaru 27 da kafuwar mulkin dimokuraɗiyya ba tare da katsewa ba.

Gwamnatin tarayya ta ba da hutu
Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo Hoto: Hon. Olubunmi Tunji-Ojo
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce hakan yana ƙunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis, 11 ga watan Yunin 2206, a birnin Abuja, ta hannun babbar sakatariya ta ma'aikatar harkokin cikin gida, Magdalene Ajani.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: An kai dattawan Arewa wuya, sun kawo mafita ga Shugaba Tinubu

Gwamnatin tarayya ta ayyana lokacin hutu

Ajani ta ce Ministan harkokin cikin gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya ayyana ranar a madadin gwamnatin tarayya, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.

Tunji-Ojo ya sake jaddada alƙawarin gwamnatin tarayya na kiyaye manufofin dimokuraɗiyya, bin doka da oda, nuna gaskiya, riƙon amana, da kuma shugabanci mai tafiya da kowa.

Ya tabbatar da cewa ma'aikatar, tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro da abin ya shafa, za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace wajen wanzar da tsaro da kuma ƙarfafa tsaron cikin gida na Najeriya.

Minista ya ba 'yan Najeriya shawara

Ministan ya lura cewa amintaccen yanayi mai karko yana da muhimmanci ga dimokuraɗiyya da cigaban ƙasa.

Ya buƙaci 'yan Najeriya da su kalli ranar hutun a matsayin wata dama ta yin tunani a matsayinsu na 'yan kasa.

“Yayin da muke bikin wannan rana ta tarihi, ana ƙarfafa kowane ɗan Najeriya da ya ci gaba da kasancewa mai bin doka da oda, ya kiyaye cibiyoyin da ke rike da dimokuraɗiyyarmu, kuma ya tuna cewa ƙarfin kowace dimokuraɗiyya ya dogara ne a ƙarshe a kan halayen 'yan ƙasarta."

Kara karanta wannan

Fada ya barke tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga a Kaduna, an kashe manyan jagorori 4

- Dr Olubunmi Tunji-Ojo

An ba da hutun ranar dimokuradiyya
Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo a ofis Hoto: Hon. Olubunmi Tunji-Ojo
Source: Twitter

Muhimmancin ranar 12 ga watan Yuni

Ya kuma ce ranar 12 ga watan Yuni na kowace shekara ta kasance rana mai muhimmanci a tarihin Najeriya domin girmama jajircewa, juriya, da sadaukarwar da 'yan Najeriya suka yi, waɗanda ƙoƙarinsu ya sa shugabancin dimokuraɗiyya ya yiwu.

"Tarihin da suka bari na ci gaba da bayyana ƙima da nauyin da ke wuyan ƙasar Najeriya."

- Dr. Olubunmi Tunji-Ojo

Gwamnatin tarayya za ta biya 'yan kwangila

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta hannun ma'aikatar kuɗi da tattalin arziki ta amince a fara biyan hakkokin 'yan kwangila na cikin gida wadanda suka biyo gwamnati.

Ma'aikatar kudin ta bayyana cewa ta amince da biyan kuɗaɗe ga 'yan kwangila fiye da 1,240 a sassan ma'aikatun gwamnati, hukumomi, da rassan gudanarwa.

An bayyana cewa amincewar ta biyo bayan wani shirin tantancewa da daidaitawa domin tabbatar da basussukan da aka biyo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng