"Me Kuma Suke So"; Ana Neman Tunzura Jagoran NDC kan Tikitin Obi da Kwankwaso a 2027
- Jagoran jam'iyyar NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson, ya dauko batun tikitin takara da Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suka samu
- Sanata Seriake Dickson ya bayyana cewa ba a karbi ko sisin kwabo ba domin mika tikitin takarar ga manyan 'yan siyasar biyu.
- Jagoran na NDC ya nuna cewa jam'iyyar ta yi wa Peter Obi da Kwankwaso riga da wando ta hanyar ba su tikitinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jagoran NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson, ya yi magana kan tikitin takarar da jam'iyyar ta ba Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.
Sanata Dickson ya ce jam'iyyar ba ta karɓi kuɗi daga hannun Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso ba kafin ta amince da su a matsayin 'yan takararta na shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa ba.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta kawo rahoton cewa jagoran na NDC ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai, ranar Alhamis, 11 ga watan Yunin 2026 a Abuja.
An ba Obi da Kwankwaso tikitin NDC kyauta
Dickson ya ce shugabancin NDC ya ɗauki shawarar ba su tikitin takarar jam'iyyar ne ba tare da gudanar da zaɓen fitar da gwani ko neman gudunmawar kuɗi ba.
“Muna farin ciki da kasancewarku a nan. Wannan jam'iyya tamu ce baki ɗaya. Yanzu su ne, bisa shawarar da wannan jam'iyyar ta ɗauka, 'yan takararmu. Kuma ba mu da wata matsala da kowane ɗayansu.”
- Sanata Seriake Dickson
Tsohon gwamnan na jihar Bayelsa ya ce jam'iyyar ta kai zuciya nesa ta hanyar ba Obi tikitin takarar shugaban ƙasa da kuma ba shi damar zaɓar mataimakin da yake so, jaridar The Punch ta kawo labarin.
“Idan har ni ne nake takara, ko kai kanka kake takara, kuma aka ba ka takarar shugaban ƙasa da mataimakin da kake so, shin jam'iyyar ba ta yi maka komai ba?”
“Mu kasance masu gayawa kanmu gaskiya yanzu. Babu wani zaben fitar da gwani da aka yi.”
- Sanata Seriake Dickson
Shin NDC ta karbi kudin Obi, Kwankwaso?
Dickson ya ce shi ko wani shugaban jam'iyya bai taɓa neman ko karɓar kuɗi daga hannun Obi da Kwankwaso ba domin ba su tikitin takarar.
“Kamar yadda na faɗa jiya da daddare, ni, ko shugaban jam'iyya, babu wani mutum a nan, da ya nemi ko karɓar kowane kuɗi daga gare su domin amincewa da shigowarsu jam'iyyar."
“Ba a nemi ko karɓar ko kwabo daga gare su ba kafin a tsayar da su 'yan takarar shugaban ƙasa daya tilo da mataimakinsa.”
- Sanata Seriake Dickson

Source: Facebook
Jagoran NDC ya kare sukar da ake yi
Dickson ya koka kan ci gaba da sukar da ake yi wa NDC duk da abin da ya siffanta da amincewarta na bayar da tikitin shugaban ƙasa ba tare da fafatawa ba.
“Me kuma mutane suke so? A wannan matakin, ya kamata mu kasance muna aiki tare don tsara yadda za a kaddamar da kamfen."

Kara karanta wannan
"Suna da amfani": Jagoran NDC ya fadi makomar Kwankwasiyya da Obidents a jam'iyyar
- Sanata Seriake Dickson
Ya ƙarfafa gwiwar mambobi da magoya bayan NDC da su maida hankali kan shirye-shiryen zaɓen 2027 maimakon saɓani na cikin gida, inda ya jaddada cewa shugabancin jam'iyyar ya ci gaba da jajircewa wajen goyon bayan tikitin shugaban ƙasarta.
An samu kura-kurai a zaben NDC
A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran NDC na kasa, Henry Seriake Dickson ya amince cewa an samu wasu kura-kurai a zaɓukan fitar da gwani a jam'iyyar.
Jagoran jam'iyyar ya kuma tabbatar da cewa an samu wasu matsaloli da kura-kurai a yayin gudanar da zaɓubbukan fitar da gwanin.
Ya ce jam’iyyar tana fuskantar ƙalubale ne saboda ƙarancin lokacin da aka ba ta duk da kasancewarta sabuwa da za ta fafata a 2027.
Asali: Legit.ng

