Arewa Ta Yi Rashi, Mai Martaba Sarkin Gabas Ya Rasu

Arewa Ta Yi Rashi, Mai Martaba Sarkin Gabas Ya Rasu

Hakimin Gwandu, Alhaji Muhammadu Rasheed, wanda aka fi sani da Sarkin Gabas, ya rasu a ranar Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

An tsara gudanar da sallar jana’izarsa da ƙarfe 3:00 na rana a fadar Sarkin Gwandu da ke Birnin Kebbi

Gwamna Nasir Idris, wanda ke halartar Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya a Amurka, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga Kebbi

Birnin Kebbi - Allah Ya yi wa Hakimin Gwandu na Jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Rasheed, wanda aka fi sani da Sarkin Gabas, rasuwa.

An tabbatar da rasuwar ne ranar Laraba, 23 ga watan Satumban 2026 ta bakin Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Kebbi, Ahmed Idris, da Mai ba Gwamna shawara kan Harkokin Sadarwa da Dabaru, Abdullahi Idris.

Za a yi jana’iza a fadar Sarkin Gwandu

Abdullahi Idris ya ce Sarkin Gabas ya rasu ne a ranar Laraba, inda za a gudanar da sallar jana’izarsa da ƙarfe 3:00 na rana a fadar Sarkin Gwandu da ke Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya yi alhini da Allah ya yi wa tsohon shugaban hukumar alhazai rasuwa

“Mai martaba ya rasu a yau, kuma za a yi sallar jana’izarsa a fadar Sarkin Gwandu da ke Birnin Kebbi da ƙarfe 3:00 na rana. Allah Ya ji kansa.”

Ya bayyana cewa marigayin ya gaji mahaifinsa, marigayi Alhaji Muhammadu Bashar Mai-Wurno, wanda shi ne babban ɗan marigayi Sarkin Gwandu, Alhaji Haruna Rasheed.

Gwamna Nasir Idris ya yi jimamin rasuwar

Shi ma Ahmed Idris ya tabbatar da rasuwar, yana mai bayyana ta a matsayin babban rashi ga Jihar Kebbi da kuma masarautun gargajiyar jihar.

Ya ce Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, wanda a halin yanzu yake ƙasar Amurka domin halartar Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya tare da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kaɗu matuƙa da labarin rasuwar hakimin.

A cewarsa, rasuwar Hakimin Gwandu babban rashi ne ga Jihar Kebbi da kuma tsarin masarautun gargajiya.

“Rasuwar Hakimin Gwandu babban rashi ne ga Jihar Kebbi da kuma masarautun gargajiya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa Gwamna Nasir Idris ya shiga jimami bayan samun labarin rasuwar Sarkin Gabas ba zato ba tsammani.

An yi addu’ar Allah Ya ji kansa

Mai taimaka wa gwamnan ya roƙi Allah Ya gafarta wa marigayin kurakuransa, Ya kuma ba shi Aljannatul Firdaus.

Ya kuma roƙi Allah Ya bai wa iyalan marigayin, al’ummar Gwandu da daukacin al’ummar Jihar Kebbi ƙarfin jure wannan babban rashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng