Daga Dawowa Najeriya, Tinubu na Fuskantar Barazana kan Tsadar Fetur

Daga Dawowa Najeriya, Tinubu na Fuskantar Barazana kan Tsadar Fetur

  • Ma’aikatan gwamnati sun sake tabbatar da wa’adin ranar 30 ga Satumba da suka bai wa gwamnatin tarayya kan tsadar fetur da sauran matsalolin tattalin arziki
  • Ƙungiyar JNPSNC ta ce idan gwamnati ba ta rage farashin fetur zuwa N500 kan lita ba, ta amince da tallafin albashi da sauransu ba, za ta fara yajin aikin gargadi
  • Ma’aikatan sun ce za su shiga yajin aikin na kwana uku daga ranar 2 ga Oktoba, 2026, idan gwamnati ta kasa ɗaukar matakan da suka nema kafin cikar wa’adin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ma’aikatan gwamnati ƙarƙashin Ƙungiyar Majalisar Tattaunawar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (JNPSNC) sun sake tabbatar da wa’adin ranar 30 ga Satumba da suka bai wa gwamnatin tarayya kan tsadar fetur da tallafi.

Kara karanta wannan

Akwai kura: Shugaban APC ya hango matsalar da Arewa za ta shiga idan Tinubu bai zarce ba

Ƙungiyar ta ce ta shirya tsunduma yajin gargadi na kwanaki uku daga ranar 2 ga Oktoba idan gwamnati ba ta rage farashin fetur zuwa N500 kan lita ba tare da ɗaukar wasu matakan rage wa ma’aikata da jama’a wahala ba.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a ofis. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Abin da ma’aikatan suka nema

Punch ta wallafa cewa JNPSNC, wadda ta ƙunshi ƙungiyoyin ma’aikatan gwamnati guda takwas, ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya ta sanar da tallafin albashi ga ma’aikata tare da fara tattaunawar sabon mafi ƙarancin albashi.

A wata wasiƙa da ƙungiyar ta aika wa Shugaba Bola Tinubu ranar 21 ga Satumba, ta nemi a fara tattaunawar mafi ƙarancin albashi da ba zai gaza N500,000 ba daga shekarar 2027.

Ƙungiyar ta ce ta tattara ma’aikatan gwamnati a faɗin ƙasar domin shiga yajin aikin gargadin idan gwamnati ta kasa magance buƙatunta kafin wa’adin da aka sanya.

An nemi a rage farashin fetur

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, 29 ga Satumba, Sakatare Janar na Ƙungiyar Ma’aikatan Gwamnatin Najeriya, Gbenga Olowoyo, ya ce wa’adin ranar 30 ga Satumba bai canza ba.

Ya ce rage farashin fetur zuwa N500 kan lita na daga cikin muhimman buƙatunsu, inda ya nemi gwamnati ta samar da wani asusun tallafi domin rage kuɗin shigo da man da kuma tallafa wa masu aikin sarrafa fetur.

Kara karanta wannan

Matsin da ake ciki yana damun Tinubu, ya fadi hanyar tsame mutane miliyan 5 daga talauci

Ana sayar da man fetur a gidan mai
Ana sakawa mota man fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya kuma nemi gwamnati ta tabbatar da sayar da ɗanyen mai ga matatar Dangote da sauran ƙananan matatun mai cikin sharuddan da za su taimaka wajen ƙara tace man fetur a cikin gida.

A cewar ƙungiyar, farashin fetur da ya kai tsakanin N1,450 da N2,000 a wasu wurare, har N2,500 a wasu yankunan da ke wajen manyan birane, yana ƙara matsin lamba kan ma’aikata da iyalansu.

Vanguard ta rahoto cewa JNPSNC ta ce idan ba a magance batun farashin fetur da tallafin albashi zuwa ranar 30 ga Satumba ba, ma’aikatan gwamnati za su fara yajin aikin gargadi na kwana uku daga ranar 2 ga Oktoba.

Korafi kan albashin ma'aikata

A wani labarin, mun ruwaito cewa Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya ce mafi ƙarancin albashin N70,000 bai isa ya tunkari matsin tattalin arzikin da ma’aikatan Najeriya ke fuskanta ba.

Keyamo ya bayyana hakan ne a taron ƙasa na shekarar 2026 kan shirin ritaya, inda ya ce tsadar rayuwa ta rage ƙarfin sayen ma’aikata, tare da kira ga gwamnati da ƙungiyoyin ƙwadago su cimma matsaya kan albashi.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, shi ma ya nemi gwamnati ta yi amfani da ƙarin kuɗaɗen da ake samu daga hauhawar farashin man fetur da ɗanyen mai wajen rage wa ma’aikata da sauran ’yan Najeriya matsin tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng