Bam Ya Tarwatse da Bayin Allah a Zamfara, Mutane da Dama Sun Rasa Rai

Bam Ya Tarwatse da Bayin Allah a Zamfara, Mutane da Dama Sun Rasa Rai

  • An samu aukuwar fashewar bam a jihar Zamfara bayan wata mota ta taka shi a kan hanyar Bagega zuwa Anka
  • Fashewar da ta biyo taka bam din ta jawo asarar rayukan bayin Allah tare da raunata wasu mutane bakwai da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
  • Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta tura karin jami'ai domin tabbatar da tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - An tabbatar da mutuwar kusan mutane 10 yayin da wasu bakwai suka ji rauni biyo bayan fashewar wani bam da aka binne a Zamfara.

An dasa bam din ne a kan hanyar Bagega zuwa Anka da ke karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara, wanda wata mota ta taka.

Bam ya tashi da mutane a Zamfara
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta kawo rahoton cewa lamarin fashewar bam din ya auku ne a ranar Talata, 9 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: 'Yan fansho sun yi dana sanin tara wa gwamna kudin sayen fam

Bam ya tarwatse da mota a Zamfara

Lamarin ya auku ne lokacin da wata motar ƙirar Volkswagen Golf 3 Wagon mai ɗauke da fasinjoji daga Bagega zuwa Anka ta taka bam din, wanda ake zargin 'yan bindiga da ke gudanar da ayyukansu a yankin ne suka dasa shi.

DSP Yazid Abubakar, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba, 10 ga watan Yunin 2026 cewa mutum ɗaya ne ya mutu sannan mutane bakwai suka ji rauni a fashewar.

Kakakin 'yan sandan ya ce rundunar, biyo bayan rahoton fashewar, ta tura kwararrun dakarun ta na musamman zuwa wurin da abin ya faru domin tantance yanayin da ake ciki.

An gano karin gawarwarki

A cewar Zagazola Makama, rundunar ta ce an gano ƙarin gawarwaki tara a wurin da abin ya faru ta hannun dakarun 'yan sandan a lokacin da ake ci gaba da ƙoƙarin bincike da kwashe gawarwakin.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Amurka ta jefa makamai,an hallaka jami'an kasar Indiya

Rahotanni sun ce fashewar ta auku ne tsakanin garuruwan Tungar Kudaku da Bagega da ke kan hanyar, wanda hakan ya sa jami'an tsaro suka mayar da martani cikin gaggawa.

Wata majiyar 'yan sanda ta bayyana cewa:

“Biyo bayan tura jami'an tsaro zuwa yankin da abin ya shafa, an gudanar da bincike mai zurfi, wanda ya kai ga gano ƙarin gawarwaki tara daga wurin da fashewar ta auku."

An rawaito cewa an kwashe gawarwakin da aka gano zuwa asibiti domin gudanar da binciken gawa da sauran hanyoyin da suka dace kafin a miƙa su ga iyalansu don birne su daidai da koyarwar addinin Musulunci.

Mutane sun mutu bayan fashewar bam a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan sanda sun tsaurara tsaro

Hukumomin 'yan sanda sun ce an ƙarfafa matakan tsaro a kan hanyar Anka zuwa Bagega domin kare aukuwar wasu abubuwan a nan gaba da kuma tabbatar da tsaro ga masu amfani da hanyar.

Sun ƙara da cewa an tsananta sintiri a kan hanyar a matsayin ɓangare na ƙoƙarin inganta tsaro da kuma dakile ayyukan masu laifi.

Sojoji sun cafke jagoran 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin sun yi dabarar cafke wani kasurgumin jagoran 'yan bindiga, Kachalla Halilu a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Dalibai mata sun diro daga bene da wasu miyagu suka kai hari kwalejin lafiya a Najeriya

Dakarun sojojin na Najeriya sun samu nasarar kama Kachalla Halilu ne a kasuwar Shinkafi da ke jihar Zamfara bayan samun bayanan sirri.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa dakarun sun tura jami’ansu zuwa kasuwar Shinkafi bayan hango Kachalla Halilu tare da kama shi ba tare da ya nuna wata turjiya ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng