Babbar Magana: Abin da Zai Faru idan Amurka Ta Sake Kaddamar da Yaki kan Iran

Babbar Magana: Abin da Zai Faru idan Amurka Ta Sake Kaddamar da Yaki kan Iran

Rundunar Sojin Ruwa ta IRGC ta yi barazanar kai wa jiragen ruwan yaƙin Amurka hari idan Washington ta sake ƙaddamar da wani yaƙi da Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wani babban jami’in IRGC ya ce Iran za ta iya kai hari kan jiragen Amurka har cikin Tekun Indiya idan sabon rikici ya ɓarke

Barazanar ta zo ne yayin da rashin jituwar Iran da Amurka kan mashigin Hormuz ke ci gaba, duk da raguwar faɗan da ake yi a 'yan makonnin nan

Birnin Tehran, Iran - Rundunar Sojin Ruwa ta Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) ta Iran ta yi barazanar kai hare-hare idan har aka sake kaddamar da yaki kan kasar.

Rundunar ta yi barazanar kai wa jiragen ruwan yaƙin Amurka hari, ciki har da waɗanda ke cikin Tekun Indiya, idan Washington ta ƙaddamar da wani sabon yaƙi da Tehran.

Mataimakin shugaban ɓangaren siyasa na Rundunar Sojin Ruwa ta IRGC, Ali Mohammadi, ne ya bayyana hakan, kamar yadda tashar Aljazeera ta ruwaito.

Kara karanta wannan

ACF: An fara wayar da kan 'yan Arewa a Kano kan sayen hannun jari a matatar Dangote

“Za mu kai wa jiragen Amurka hari”

Mohammadi ya ce idan Shugaban Amurka Donald Trump yana ganin cewa Mashigar Hormuz mallakarsa ne, to ya kamata jiragen ruwan Amurka su kasance a yankin.

“Idan Trump yana ɗaukar Mashigar Hormuz a matsayin mashigarsa, to me ya sa jiragen ruwansa da sauran jiragen ruwa ba sa nan?” in ji Mohammadi.

Ya ƙara da cewa idan Amurka na ikirarin cewa tana da iko da hanyar ruwan, to ya kamata ta turo jirginta kusa da yankin.

Mohammadi ya kuma yi gargadin cewa idan wani sabon yaƙi ya ɓarke, Iran za ta kai hari kan jiragen ruwan Amurka.

“Idan wani yaƙi ya sake ɓarke wa, babu shakka za mu kai wa jiragen ruwansu da masu lalata jiragen ruwa hari, har ma a cikin Tekun Indiya.”

Rikici kan Mashigin Hormuz

Wannan barazana ta zo ne a lokacin da ake ci gaba da samun ɗimbin rashin jituwa tsakanin Iran da Amurka bayan watanni na fuskantar juna ta fuskar soji a yankin Tekun Farisa da Mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Trump ya kawo babbar matsala bayan Iran ta mika tayin buɗe Hormuz ga Amurka

Mashigar Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin ruwa da ake amfani da su wajen jigilar man fetur a duniya.

A 'yan makonnin nan, jami’an sojin Iran sun sha ƙalubalantar ikirarin Trump na cewa Amurka tana da “cikakken iko” kan Mashigar Hormuz.

Mohammadi ya ce ikirarin Washington bai yi daidai da halin da ake ciki a yankin ba, yana mai gargadin cewa dakarun Amurka za su fuskanci martanin rundunar sojin ruwan Iran idan suka kusanci mashigin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng